2019: Buhari na jiran tabbatar ma sa da nasararsa

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari na Jam'iyyar APC na jiran tabbatar da nasarar sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon jihohi 36 da aka bayyana ya nuna Buhari ya ba babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ratar kuri'a sama da miliyan hudu.
Zuwa yanzu Atiku yana da yawan kuri'a 11,262,978, bayan kammala tattara sakamakon dukkanin jihohin Najeriya.
Tuni dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon, wanda ta kira aringizon kuri'u saboda ya saba wa sakamakon da tattara daga wakilanta.
Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta yi Allah-wadai da matakin da PDPn ta dauka.
A shekarar 2015 aka fara zabar Shugaba Buhari bayan da ya kayar da shugaba mai ci a lokacin, Goodluck Jonathan, na PDP.
Jam'iyyar ta PDP ta shafe shekara 16 tana da mulkar Najeriya.
Kuma Buhari ne ya zamo dan siyasar adawa na farko da ya lashe zabe a kasar.
Yaya zaben yake aiki?

Dan takarar da ya fi samun kuri'u ake ayyanawa a wanda ya yi nasara a zagayen farko, in dai har ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin kasar.
'Yan takarar shugaban kasa 73 ne suka yi rijista, amma an fi yin gwagwarmaya ne tsakanin Buhari da Atiku.
Dukkansu sun fito ne daga arewacin kasar inda Musulmai suka fi yawa, kuma dukkansu sun haura shekara 70, yayin da mafi yawan 'yan kasar da suka yi rijistar zabe 'yan kasa da shekara 35 ne.
Wadanne ne manyan batutuwan?
Najeriya ce kasar da ta fi kowacce arzikin man fetur a Afirka, amma cin hanci da gazawa wajen zuba jari ya sa abun da ake samu daga arzikin ya jawo matukar ci baya.
Farfadowar da har yanzu kasar ke yi daga koma bayan da tattalin arzikinta ya samu a 2016 na nufin babu isassun ayyukan yi ga dumbin matasan da ke fafutukar neman aiki.
Kusan kashi daya bisa hudu na matasan kasar ba su da aikin yi.

Zaben cikin alkalumma
- Masu katin zabe mutum miliyan
- Kashi 51 cikin 100 na masu kada kuri'a 'yan kasa da shekara 35
- 'Yan takarar shugaban kasa 73 ne
- Rumfunan zabe 120,000















