Malam Shekarau ya zama Sanata

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya lashe kujerar sanata a Kano ta tsakiya.
Shekarau na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 506,276 inda ya kada abokin hammayarsa na jam'iyyar PDP Ali Madaki wanda ya samu kuri'a 29,775.
A hirarsa da BBC bayan sanar da sakamakon zaben, Shekaru ya ce babu wani sanata a Najeriya da ya samu yawan kuri'unsa.
Ya kuma yi watsi da zargin cewa ba zai goyi bayan Buhari ba a majalisa dattawa, yana mai cewa Mahasadda ne ke son hada shi da Buhari.
Tsohon gwamnan ya ce zai ba shugaba Buhari cikakken hadin kai musamman wajen tabbatar da sasanci tsakanin bangaren majalisa da bangaren shugaban kasa.







