Wani ya kwace akalar jirgi da bakin bindiga a Bangladesh

Asalin hoton, AFP
An tabbatar da cewa wani fasinjan da ya yi garkuwa da mutane tare da barazanar ragargaza jirgin da yake ciki wanda ya tashi daga birnin Dhaka na Bangladesh yana dauke ne da bindigar roba
'Yan sanda sun harbe mutumin mai shekara 25 bayan da jirgin ya yi saukar gaggawa.
Dukkan fasinjoji 148 da ke cikin jirgin na Birman Airlines mai lamba BG147, sun yi ta kansu bayan saukar jirgin a birnin Chittagong.
Daga baya jami'ai sun ce mutumin ba shi da cikakkiyar nutsuwa kuma ya so ya yi magana da firai minista.
A wani aiki da suka kaddamar na tsawon minti 10, dakaru na musamman na Bangladesh sun dira cikin jirgin tare da harbe mutumin, wanda aka ce sunansa Mohammad Palash Ahmed.
Ana fargabar cewa yana dauke ne da abubuwan fashewa a jirgin mallakin wani kamfanin Dubai, kuma wasu fasinjojin sun ce sun ganshi dauke da bindiga.
Amma kwamishinan 'yan sanda na Chittagong Kusum Dewan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya ce mutumin na dauke ne da bindigar wasan yara kuma ba ya dauke da wani abun fashewa.

Asalin hoton, EPA
Wani kwamanda Sarwar-e-Zaman, wanda shi ne manajan filin saukar jiragen ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Ahmed ya so ya yi magana da firai ministan Bangladesh, wanda ke ziyara a birnin Chittagong na gabar teku, saboda matsalolin da yake fuskanta a aurensa.
Mista Zaman ya ce: "Dalilan da ya baya na kwace akalar jirgin su ne cewa yana da matsala da matarsa don haka yana son yin magana da firai minista Sheikh Hasina."
A yanzu masu bincike na kokarin gano yadda har Ahmed ya samu wucewa cikin jirgi da bindigar roba duk da jami'an tsaro da ke wajen.
An kara tsaurara tsaro a filayen jiragen kasar da suka hada da babban filin jirgi na Hazrat Shahjalal International da ke Dhaka sakamakon faruwar wannan lamari.

Asalin hoton, AFP
Jami'an soji sun ce mutumin ya ji rauni sakamakon harbin bindigar kafin daga bisani ya mutu.
"Mun yi kokarin kama shi ko ya sadaukar da kai amma sai ya ki, sai kawai muka harbe shi," kamar yadda Manjo Janar Motiur Rahman ya shaida wa manema labarai bayan faruwar lamarin.
"Dan Bangladesh ne. Bindiga kadai muka samu a jikinsa."
Ma'aikatan jirgin ne suka nuna damuwa bayan da aka ce mutumin yana nuna wasu alamu na rashin gaskiya da kuma nuna alamar niyyar kwace akalar jirgin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fada.
Ba a bata lokaci ba wajen zagaye tare da hana mutane kusantar jirgin bayan saukarsa a filin jirgin Shah Amanat da ke Chittagong, yayin da jami'ai suka yi kokarin yin magana da mutumin.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna cincirindon mutane a filin jirgin kusa da jirgin samfurin 737-800.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X











