Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amsar tambayoyinku kan zaben Najeriya na 2019
Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci mabiyanmu da masu saurare su aiko da tambayoyinsu kan abin da suke son sani game da zaben Najeriya.
BBC Hausa ta mika tambayoyin da aka aiko ga Mallam Aliyu Bello, kakakin Hukumar zabe Najeriya, INEC, wanda kuma ya yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.
Shin INEC ta yi karin rumfunan zabe?
INEC ta samar da karin wuraren da 'yan Najeriya za su jefa kuri'a, amma karkashin rumfunan zaben da ake da su ba tare da kirkiro wasu sabbi ba.
An kara fadada rumfar zabe zuwa rassa domin saukake wa masu zabe, inda za a iya tantance mutum uku a lokaci daya cikin sauki maimakon cunkushewa a rumfa daya.
Amma INEC ta ce ba wai an kara rumfa ba ne ko an canza rumfa ba.
Za a tattara sakamakon ne a waje daya a gabatar da shi a matsayin rumfa daya.
Idan aka ga layuka biyu ko uku a rumfa daya kada a zata na bugi ne, INEC ce ta kirkiro da su a matsayin rumfa daya domin sawwake zabe ba tare da canza rumfar da aka sani ba.
An kirkiro da su ne domin yadda mutum biyu ko uku ko hudu za su yi zabe a lokaci daya cikin sauki.
Rumfunan da ake da su suna nan ba a canza ba, amma an samar da kananan rumfuna karkashin babbar rumfa domin saukake zabe.
An yi haka ne saboda karuwar masu kada kur'a a rumfa daya.
A yanzu akwai rumfar zabe dubu 119, 974.
Saboda ba a samu karin rumfuna ba, ya sa hukumar zabe ta samar da wasu kananan rumfuna karkashin rumfa daya.
Malaman zabe nawa ne a rumfar zabe?
Ko wace rumfar zabe tana da jami'an zabe guda hudu, kuma ko wane jami'i aikinsa daban, wadanda za a gansu sanye da wasu tufafin da ke tabbatar da jami'an zabe ne.
Akwai wanda aikinsa kawai tantance katin masu zabe ne a rumfa daya. Wannan zai magance matsalar yadda mutane ke yin cincirindo a rumfa ba tare da sanin ba a nan ya kamata su yi zabe ba.
Jami'i na biyu shi zai kula da na'urar card reader da ke tantance masu zabe.
Jami'i na uku kuma aikinsa shi ne diba sunan masu jefa kuri'a a kundin rijista a rumfar zabe. Kuma aikinsa ya kunshi sake diba suna da yin maki ga wanda ya zo zabe tare da shafa wa mai jefa kuri'a tawada.
Jami'i na huku shi zai yagi takadar kuri'a ya ba mai jefa kuri'a, yayin da shi kuma mai jefa kuri'a zai ta fi inda aka killace domin dangwala kuri'a da kada wa a cikin akwati.
Baya ga jami'an zabe a rumfa akwai kuma babban jami'i da ke kula da rumfunan zabe guda 10 wanda idan akwai wata matsala shi zai kawo cikin gaggawa ba tare da an tafi babban ofishin hukumar zabe ba.
Shin za a yi amfani da 'card reader'?
Za a yi amfani da na'urar tantance masu zabe da ake kira card reader a zaben 2019 Kamar yadda aka yi amfani da ita a zaben 2015.
INEC yin amfani da card reader a zabe wajibi ne domin an yi amfani da ita kuma an ga amfaninta.
Hukumar ta ce an kara inganta na'urar fiye da wadanda aka yi amfani da su a zaben 2015.
Kuma wadanda za a yi amfani da su sun fi aiki cikin hanzari fiye da na 2015.
Wane tanadi aka yi wa tangardar na'ura?
Idan card reader ta kakare ta daina aiki, Hukumar zabe ta ce ta yi tanadin matakai biyu.
Mataki na farko shi ne an amince nan take a nemi wata na'urar a ci gaba da aikin zabe idan akwai sauran lokaci.
Hukumar ta ce dukkan runfa 10 akwai wakilanta da ke yawo da na'urar card reader na shirin ko-ta-kwana idan har wadanda ake amfani da su sun kakare.
Za a iya sanar da babban jami'an hukumar domin maye gurbin na'urar da ta kakare.
Mutum zai iya zabe idan na'ura ta ki karbar yatsansa. INEC ta ce ta fito da tsari ga wadanda na'ura ta ki karbar yatsansu.
Idan har aka tabbatar da sunan mai zabe ne a kundin rijista za a ba shi dama ya jefa kuri'arsa, tare da tare da rubuta lambar wayarsa a kudin masu zabe.
Hukumar ta ce rijistar zabe da ke dauke da hoto da sunan mai zabe da kuma wakilan jam'iyyu ne za su tabbatar da mutumin da na'ura ta ki karbar yatsansa.
Amma idan har lokaci ya kure ba a maye gurbin card reader da ta daina aiki ba kuma ba tantance mutane da dama ba, an yarda a dage zabe a wannan rumfa har zuwa washegari wato lokacin da aka samar da wata na'urar.
Tanadin da aka yi wa masu bukata ta musamman
An yi tanadin yadda makafi za su kada kuri'a ta hanyar samar da takardarsu ta zabe ta daban da kuma abin da suka saba rubutu da shi da ake kira 'braile' a turance.
Za su dorar braile din ne a takardar zabe, kuma an samar da ita ta yadda za su iya shafa wa su gano jam'iyyar da za su dangwala wa.
Ga masu lalurar makanta da ba su yi karatu ba, hukumar INEC ta ce za su iya zuwa da jagora daga gida a wajen zabe.
Hukumar ta ce ba a yadda daya daga cikin jami'anta a rumfar zabe ba su yi wa mai lalurar makanta jagora ba.
An kuma yi tanadin wani babban gilashi a rumfar zabe ga zabaya masu lalurar gani, wadanda idan rana ta yi sosai ba su iya gani ba. Don haka an yi tanadin gilashin da zai kara girman bakaken jam'iyun siyasa.
Dole ne sai an gama tantancewa za a fara kada kuri'a?
Sabanin yadda aka yi a 2015 inda sai an tantance ka sannan daga baya ka dawo ka kada kuri'a, a zaben 2019 mutum zai iya jefa kuri'arsa nan take bayan an tantance shi.
Mai jefa kuri'a da zarar ya zo an tantance shi da na'urar card reader, sai a ba shi kuri'arsa kai tsaye ya shiga ya kada wa jam'iyyar da yake so ba tare da ya yi jinkiri ba.
Da wane yatsa ne za a dangwala kuri'a?
Masu zabe za su iya amfani da kowane yatsa yayin dangwala kuri'arsu.
Amma mai zabe zai tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam'iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam'iyyar daban.
INEC ta karyata wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta musamman WhatsApp cewa hukumar ta canza tsarin yadda mutane za su jefa kuri'a.
Hukumar zaben ta ce babu yatsan da aka ce dole sai shi za a yi amfani da shi, masu zabe za su iya amfani da kowane irin yatsa su dangwala kuri'arsu.
Ko an yarda a jira a fadi sakamako a rumfa?
Mutum yana da zabin ya tsaya ya jira bayan ya jefa kuri'arsa domin ganin abin da zai wakana a rumfarsa ko kuma yana da zabin ya koma gida ya kwanta.
Mai zabe yana da damar ya tsaya ya saurari sakamakon zaben rumfarsa don ya zama shaida.
Amma wakilan jam'iyyu ne ke da hakkin raka sakamakon zabe zuwa cibiyar da ake tattara sakamakon zaben gaba daya inda za su mika wa wakilansu da ke babbar cibiyar.
Yaushe za a ji sakamakon zaben shugaban kasa?
Najeriya babbar kasa ce, ba a san lokacin bayyana sakamako ba sai lokacin da ko wace rumfa ta kammala zabenta kuma aka kawo sakamako
Bayyana sakamako yana da alaka ne da kammala tattara sakamakon da suka fito daga jihohi kafin bayyana wanda ya yi nasara.
Shugaban hukumar zabe ne doka ta ba 'yancin fadin sakamakon zaben shugaban kasa.
Yawan kuma rinjayen kuri'i ba shi ba ne cin zabe a Najeriya.
Dole sai dan takara ya samu kashi daya cikin hudu na adadin kuri'un da aka kada a biyu bisa uku na jimillar jihohin da aka yi zabe.
Sai dan takara ya samu daya cikin hudu na kuri'u a jihohin akalla 25 daga jihohi 36 na najeriya hadi da Abuja kafin lashe zabe.
Dan takara na iya samun rinjayen kuriu amma ta kasa cin zabe saboda gaza cika sharuddan cin zaben.
Don haka lisafin yawan kuri'u ba shi ba ne cin zabe a Najeriya.
Me za a yi da kwanten takardun zabe.
Domin kaucewa, hukumar zabe ta umurci jami'anta su soke sauran takardun zabe da suka rage wadanda ba a yi amfani da su ba don gudun aringizon kuri'u.
Wannan ne ya sa hukumar zaben ta ware wasu lambobin waya na musamman da za a tuntube a sanar da ita wata matsala, ko sayen kuri'u ko saba doka a lokacin zabe.
Lambobin su ne: 09050858699 da 070022554632 da 09084444333