Shin talauci na karuwa a Najeriya?

    • Marubuci, Daga Peter Mwai & Jack Goodman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check

Najeriya ce kasa mafi girman tattalin arziki kuma wacce ta fi ko wacce man fetur nahiyar Afirka.

Amma fiye da rabin 'yan kasar na cikin kangin talauci, kuma kashi 60 cikin 100 na mutanen dake zaune a birane ba sa iya biyan kudin hayar gidajen da suka fi arha.

Haka kuma, akwai 'yan Najeriya masu arzikin gaske kuma gibin da ke tsakanin masu arziki da talakawa a bayyane ya ke karara a manyan biranen kasar.

Gabanin zabuka a Najeriya ranar 16 ga Fabrairu, BBC ta duba kan ko talauci ya karu da kuma idan gibin da ke tsakanin masu kudi da talakawa na kara fadi.

Gwamnati ta yi ikirarin cewa ta kawar da talauci kuma ta zargi gwamnatocin da suka gabata da almundahana a bangarorin man fetur da tattalin arziki.

"Ba wai talauci ya ragu ba ne, a'a. Ina nufin abin da ke faruwa yanzu shi ne muna duba batun talauci," in ji Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.

Babban abokin karawar Buhari a zaben, Atiku Abubakar, ya ce tattalin arzikin Najeriya bai taba tabarbarewa irin na wannan karon ba.

"Tambaya mafi muhimmanci a wannan zaben ita ce: shin kun fi yadda kuke shekaru hudu da suka gabata, kun fi arziki ko kun fi talauci?"

Matsin Tattalin arziki

Sai a kwanan nan ne tattalin arzikin Najeriya ya fara nuna alamar farfadowa bayan lokaci mai tsawo yana cikin matsi.

Hukumar Kididdiga ta kasar ta ce yawan mutanen da ba su da aikin yi ya kai kashi 20 cikin 100.

Sai dai akwai rashin alkalumma na baya-bayan nan, duk da cewa ana kan tattara bayanai kan talauci a kasar.

Amma masana na ganin cewa abu ne mai wuya yanayin da talakawa ke ciki ya sauya.

"Sai dai saboda yadda yawan mutane ke karuwa da rashin ayyukan yi, da alama gibin da ke tsakanin masu hannu da shuni da marasa galihu na kara fadada," in ji Bongo Adi, wani masanin tattalin arziki a Makarantar Koyon Kasuwanci ta Legas.

Talauci ya yi mana katutu

Ana tunanin cewa rashin daidaito na kara muni a kasar.

"Najeriya na da tarihin cin hanci da rashawa da rashin bin ka'ida" hakan ya taimaka wajen karuwar mutanen da ke rayuwa cikin talauci, in ji Abdulazeez Musa, wani masani a kungiyar Oxfam.

Kan batun gibin da ke tsakanin masu hannu da shuni da marasa galihu, masanin tattalin arziki Bismarck Rewane ya yi kiyasin cewa kashi 5 cikin 100 ne kawai na jama'ar kasar suke sarrafa kashi 40 cikin 100 na arzkin kasar.

Akwai manufofin rage radadin talauci, a cewarsa, amma gwamnatocin ba da gaske suke ba wajen aiwatar da su.

Talauci ya fi yawa a jihohin arewacin kasar fiye da a jihohin kudancin kasar.

Jihar Sakkwato a yankin arewa maso yammacin kasar ita ce jihar da ta fi kowacce fadawa talauci da kaso 18 cikin dari yayin da a jihar Legas da ke kudu maso yamma ke da kaso 34 cikin dari.

Yawan talauci ya karu da kusan kashi 15 cikin dari tsakanin 2004 da 2010.

Talauci ya yi mana katutu, in ji Omolara Adesanya, wata 'yar takarar gwamna a jihar Legas.

Muhalli gwaji ne na talauci

Kusan rabin 'yan Najeriya na zaune ne a birane, amma gibin da ke tsakanin talakawa da masu kudi ya zamo abin al'ajabi- babu mutane a cikin akasarin gidajen da aka gina a unguwannin masu hannu da shuni, yayin da unguwannin marasa galihu sun cika makil da mutane.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa kashi 69 cikin 100 na mazauna birane a Najeriya na zaune ne a yanayi na talauci.

Ginawa ko sayen gida na da tsada. Ana iya kashe dala 50,000 wajen gina gida mai dauke da dakuna 3 a Najeriya, yayin da a Afirka ta Kudu da dala 36,000 za a iya gina irin wannan gidan, in ji Babban Bankin Duniya.

Talauci ko rashin daidaito?

Duk da cewa ba boyayyen abu ba ne cewa akwai rashin daidaito sosai a Najeriya, zai yi wuya a iya sanin girman lamarin saboda rashin alkalumma, in ji Zuhumnan Dapel.

A cewarsa, kasashe masu tasowa ba su damu da rashin daidaiton albashi ba kamar yadda suka damu kan rayuwa cikin talauci.

"Ko da mutane suna rayuwa cikin matsanancin talauci, babban abun damuwa shi ne fitar da su daga kangin talaucin," ya ce.

Kuma wannan shi ne babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

A cewar babban Bankin Duniya, a yanzu Najeriya ce kasar da ta fi yawan mutane masu rayuwa cikin talauci, inda har ta kere Indiya.

Bankin na kaffa-kaffa kan bayanan da za a iya dogara da su, amma ya nuna girman matsalar da kasar ke fuskanta- ga duk wanda ya yi nasarar lashe zaben da ke karatowa.

Fassarar Fauziyya Kabir Tukur