Dalilan da suka sa ASUU ta janye yajin aiki

Kofar shiga Jami'ar Lagos

Asalin hoton, Getty Images

Duk da kungiyar malaman jami'oi na kasa ASUU ta janye yajin aiki amma har yanzu jami'o'i ba su sanar da ranar da dalibansu za su fara karatu ba.

Dalibai a jami'o'in na kasa da suka shafe tsawon wata uku a gida sun zura ido su ji ranar da za a kira su domin ci gaba da karatunsu.

ASUU ta tsunduma yajin aiki ne a ranar 3 ga watan Nuwamba don matsawa gwamnati lamba kan inganta albashi da kudaden alawus da kuma farfado da darajar jami'o'in na kasa.

Bayan janye yajin aikin a Alhamis, ASUU ta fadi wasu dalilai da ya sa ta janye yajin aikin.

Shugaban kungiyar Farfesa Abiodun Ogunyemi, ya ce akwai manyan bukatu takwas da suka gabatar inda gwamnati ta cimma hudu yayin da kuma ake jiran ta diba sauran hudun.

Ya kuma ce ASUU za ta koma yajin aiki idan har gwamnatin Tarayya ta ki mutunta yarjejeniyar 2017 da suka sanya wa hannu.

Bukatu hudu da aka cimma matsaya

Batu na farko shi ne, ASUU na son a tabbatar da kamfanin fansho mai zaman kansa da zai kula da kudaden fansho na malaman jami'oi wanda tuni aka samu lasisin kamfanin da ake kira NuPenco.

Kungiyar ta ce an shafe shekara 10 ana tattauna batun amma an kasa aiwatarwa.

Na biyu kuma shi ne kan batun biyan kudaden albashi da malaman jami'oi 20 ke bi.

Na uku kuma, samar da hurumi da za a hada kai tsakanin kungiyar da gwamnoni wadanda ya kamata su samar da kudi musamman domin tafiyar da jamo'in jihohi. Kungiyar ta ce an kirkiro tsarin tare da tabbatar da shi.

Batu hudu kuma shi ne kara tabbatar da bangarorin da za su ci gaba da tattaunawa da juna tsakanin bangaren kungiyar da gwamnatin tarayya domin samun karin haske kan inda gwamnati ta dosa.

Bukatun da ba a cimma matsaya ba

  • Kwamitin kai ziyara dukkanin jami'oin tarayya
  • Biyan alawus-alawus din malaman jami'a
  • Biyan kudaden alawus na malaman jami'ar Ilorin wadanda har yanzu suke bin bashi
  • Kudaden jami'oi da suke jiran gwamnati ta saki naira biliyan 25 tsakanin watan Maris zuwa Afrilun 2019.