Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mummunar fahimta aka yi wa kalaman El-Rufa’I - Buhari
Fadar shugaban Najeriya ta nuna goyon bayanta ga kalaman gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i kan barazanar da ya yi ga tsoma bakin 'yan kasashen waje ga sha'anin zaben kasar.
Gwamnan El-Rufai ya ce duk wani dan kasar wajen da ya tsoma baki a zaben Najeriya na 2019 za a koma da gawarsa.
Ya fadi haka ne a shirin Tuesday Live da ake gudanarwa ranar Talata a gidan talabijin na kasa NTA.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa sun gamsu da bayanan na gwamnan Kaduna.
"Mummunar fahimta aka yi wa kalaman da gwamnan ya yi."
"Ba ya da nufin ya nemi a raunata wani ko halaka wani, ko dan Najeriya ko dan kasar waje dangane da harakar zabe."
"Magana ce ta kare kishin kasa da mutuncin kasarsa ta Najeriya," in ji shi.
Kalaman gwamnan na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce. inda wasu suke ganin bai dace ace gwamna kamarsa ba ya fadi haka a daidai wannan lokaci da hankalin duniya ya karkata ga zaben Najeriya.
Wasu sun yi wa kalaman fassarar cewa, gwamnan yana nufin za a farwa 'yan kasashen waje da suka shigo Najeriya domin sa ido ga zaben kasar.
Amma gwamnan ya kare kalamansa inda kakakinsa Samuel Aruwan ya shaida wa BBC cewa gwamnan na nufin kasashen su mutunta 'yancin cin ganshin kan Najeriya.
Garba Shehu ya ce a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya babu inda aka yadda wata kasa ta dauki lamurran cikin gida na wata kasa ta tsoma baki ko ta yi karanbani ko kankanba akai ba.
A sanarwar da ya fara tura BBC, Garba Shehu ya ce "Mun ji kalaman da gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i ya yi kan kiran da 'yan adawa ke yi ga kasashen waje su tsoma baki ga harakokin cikin gidanmu, za mu ce ya kamata kalamansa su kawo karshen zancen. Ba wani abu ba ne da za a tada kura akai," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi kalaman ne da nufin kare manufofin kasa, kuma hakan ya nuna El Rufa'i da jam'iyyar APC da sauran 'yan takara sun yi imani da mulkin demokuradiya ta hanyar zabe.
Kuma ba za su yarda da duk wani rikici ba kan 'yan kasa da kuma baki daga kasashen waje.
Ta kara da cewa, gwamnatin Tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari za ta yi aiki tare da masu sa ido kuma ba za a taba juya masu baya ba a harakokin zaben kasar.
Sanarwar ta kuma ce, fadar shugaban kasa na tabbatar wa 'yan Najeriya da sauran al'ummar duniya cewa shugaban kasa zai yi duk abin da ya dace iya ikonsa domin tabbatar da ganin an yi karbabben zabe a fadin kasar.
"'Yan adawa ne ke neman hanyoyin da za su muzanta jam'iyyar APC da gwamnatin Buhari."
"Gaskiya ce El Rufa'i ya fito ya fada cewar babu tababar zabe za a yi na gaskiya na hakika."
"Duk kuri'a sai an kirga, kuma mai ita sai an ba shi kayansa," in ji shi.
Ya kuma ce an ba hukumar zabe cikakken hakkinta, abin da ba'a taba yi ba a tarihin Najeriya, domin ko naira daya ba su bin gwamnati daga kudaden da suka nema naira biliyan 180.
Abin da El Rufa'i ya fada
Gwamna El Rufa'i da ke amsa tambayoyi a shirin Tuesday Live da ake gabatarwa duk ranar Talata kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa ya ce "ga wadanda ke kiran wani ya shigo don ya shiga tsakani a Najeriya, muna jiransa ya zo ya shiga tsakani."
"Za a koma ne da gawarsu domin babu wanda zai shigo Najeriya ya fada muna yadda za mu tafiyar da kasarmu. Mun samu 'yancin kai."
"Muna kokarin yadda za mu tafiyar da kasarmu yadda ya kamata. Kuma mun san tarihin wadannan kasashen da suke kokarin koya muna wadannan abubuwan."
"Mun karanta tarihinsu, kuma mun san matsayin ci gabansu. sun fuskanci wadannan kalubalen. Don haka kamata ya yi mu yi aiki tare. Mu ba juna shawara amma ba su karantar da mu ba, in ji El Rufa'i.
Martanin Tarayyar Turai
Tarayyar Turai ta ce, tawagarta za ta ci gaba da aiki a sassan Najeriya kafin zaben kasar da za a gudanar makon gobe.
Sanarwar na zuwa ne bayan kalaman gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i kan 'yan kasashen waje a zaben Najeriya.
Tarayyar Turai ta ce ta tura tawagarta ne bisa abincewar gwamnatin Najeriya. Kuma ta ce duk da tsaron rayukan jami'anta nada muhimmaci, amma za ta ci gaba da aikin da aka gayyace ta.
Tawagar Tarayyar Turai da tuni ta isa Abuja, ta kunshi kwararru 11, da wasu kimanin 40 da suka kwace a aikin sa ido a zabe wadanda aka rarraba zuwa sassan Najeriya.