Amurka ta sanya takunkumin hana 'yan Ghana bisa

Visa
Bayanan hoto, Amurka ta zargi 'yan ci-ranin 7,000 da shiga kasar ba tare da izini ba

Amurka ta sanya takunkumin hana takardar izinin shiga kasa, ko bisa ga 'yan Ghana saboda kasarsu ta ki karbar 'ya'yanta 7,000 da hukumomin Amurka ke son komawa da su gida.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Accra ya ce zai takaita bisar da zai bai wa 'yan Ghana, inda zai bayar da ita ne kawai ga ma'aikatan jami'an jakadancin da aka tura Amurka.

Jami'an Amurka sun yi gargadi cewa za a iya fadada takunkumin zuwa ga wasu 'yan kasar ta Ghana idan ba a warware wannan matsala ba.

A bara, hukumomin Ghana sun nuna tababarsu kan mutanen da ake son komawa da su kasar suna masu cewa watakila ba 'ya'yansu ba ne.

A watan Satumbar da ya wuce, an ambato jakadan Ghana a Amurka, Baffour Adjei-Bawuah, yana cewa sun cimma matsaya kan komawa da mutanen kasar Ghana.

Amurka ta zargi 'yan ci-ranin 7,000 da shiga kasar ba tare da izini ba, ciki har da wuce wa'adin da aka ba su na zama a kasar.