CJN Onnoghen: Shin majalisar dattawa za ta yi zaman gaggawa?

Bukola Saraki

Asalin hoton, @bukolasaraki

Lokacin karatu: Minti 3

Akwai yiwuwar majalisar dattawan Najeriya za ta gudanar da zaman gaggawa kan batun dakatar da Alkalin Alkalan kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Sanata Ali Muhammad Ndume ya shaida wa BBC cewa duk da ba su samu sanarwa a hukumance ba amma sun ji cewa shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki ya kira zaman gaggawa a ranar talata.

Ya ce a ranar Litinin ne sanatocinsu na jam'iyyar APC a majalisar za su tattauna kafin zaman majalisar na gaggawa a ranar Talata.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda yake neman wani wa'adi, ya dakatar da Alkalin Alkalan Walter Onnoghen a ranar Juma'a game da zarge-zargen saba dokokin bayyana kadarori.

Kotun da'ar ma'aikata ce ta bayar da umarni a dakatar Onnoghen har sai an kammala shari'arsa.

Batun dakatar da Alkalin Alkalan kasar Walter Onnoghen tare da nada Ibrahim Tanko a matsayin na riko da shugaba Muhammadu ya yi ya haifar da ce-ce-ku-ce da matsin lamba a ciki da wajen Najeriya.

Kuma ana kyautata zaton batun dakatar da Alkalin Alkalan ne zai mamaye zaman majalisar da jam'iyyar adawa ta PDP ke jagoranta.

Tun da farko a cikin wasu jerin sakwanni da ya tura a Twitter, shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ya yi gargadi ga shugaba Buhari ya janye matakin dakatar da Alkalin Alkalan.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Saraki wanda shi ne shugaban yakin neman zaben Atiku, ya ce dakatar da Alkalin Alkalan ya sabawa bangaren shari'a da kuma kundin tsarin mulki.

Ya kuma yi gargadin cewa za su dauki mataki idan har shugaban ya ki mutunta tsarin da ya dace wajen cire Alkalin Alkalan.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

PDP ta dakatar da yakin neman zabe

Bukola Saraki tare da Dino Melaye

Asalin hoton, @bukolasaraki

Bayanan hoto, An dade ana takun-saka tsakanin majalisa da bangaren zartarwa a Najeriya

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta dakatar yakin neman zabenta na tsawon kwana uku domin adawa da matakin dakatar da Alkalin Alkalan kasar yayin da ya rage makwanni a gudanar da babban zabe.

PDP ta shaida wa BBC cewa tana son Shugaba Buhari ya janye matakin, yayin da kuma kungiyar lauyoyi ta ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulki.

A wani sakon twitter da ya wallafa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka ga Buhari inda ya kira mulkinsa na "kama-karya kan yaki da yake da bangaren shari'a"

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Kasashen duniya sun damu

Shugaban Najeriya Muhammadu

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Buhari ya nada Alkalin Alkalai na riko mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad

Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka sun bayyana damuwa kan cire Alkalin Alkalan, suna masu cewa matakin zai iya zama matsala ga zaben kasar.

Tawagar masu sa ido ta tarayyar Turai a zaben Najeriya ta yi kira ga dukkanin bangarori na siyasa su bi tsarin doka da kundin tsarin mulki ya tanadar.

Amurka da Birtaniya sun nuna damuwa ne kan yadda aka dakatar da Alkalin alkalan ba tare da amincewar majalisa ba.

Birtaniya ta ce wannan zai iya cusa shakku a ciki da wajen kasar kan muradin gudanar da sahihin zabe a Najeriya.

Amurka ta ce yadda dakatar da Alkalin Alkalan ya janyo suka game da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma 'yancin bangaren shari'a, hakan na iya kawo cikas ga alkawalin da gwamnati da 'yan takara da jam'iyyun siyasa suka yi na tabbatar da ganin an yi sahihi kuma karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.

Amma a martanin da ta mayar, fadar shugaban Najeriya ta ce ba za ta amince da abin da ta kira shishigin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidanta ba.

Ta ce a shirye ta ke ta tabbatar da an gudanar da sahihin zabe amma ba za ta amince da katsalandan daga waje ba kan harakokin da suka shafi cikin gidanta ba.