Kun san iyalan Atiku Abubakar?

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Atiku Abubakar yana takara ne a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP
    • Marubuci, Fauziyya Kabir Tukur
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Ranar Alhamis ne muka wallafa kasidar musamman game da iyalan Shugaba Muhammadu Buhari, a wannan kasidar kuma mun yi waiwaye game da iyalan babban abokin karawarsa a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyan PDP, Atiku yana da mata 3 da 'ya'ya 28.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwambar 1946 a kauyen Jada a jihar Adamawa.

Atiku ya auri matarsa ta fari Titilayo Albert a Disambar 1971 a Legas, a lokacin tana da shekara 19.

Amina Titi Atiku Abubakar

Asalin hoton, FACEBOOK/TITIABUBAKAR

Bayanan hoto, Amina Titi. 'yar asalin garin Ilesha ce a jihar Osun da ke kudancin Najeriya

Titi 'yar asalin garin Ilesa ce, a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ranar 26 ga watan Oktobar 1972 ta haifi 'yarta ta fari tare da Atiku Abubakar, Fatima.

Daga nan sai ta haifi Adamu da Halima da kuma Aminu.

Titi Abubakar dai ta zamo matar Atiku da duniya ta fi sani, don ko a lokacin da ya yi mataimakin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007 ita ce ta rike ofishin matar mataimakin shugaban kasa.

Rukaiya Atiku Abubakar

Asalin hoton, TWITTER/@RukaiyaAtiku

Bayanan hoto, Rukaiya, daya daga cikin 'ya'yan Atiku Abubakar

Kuma sun samu jituwa sosai tsakaninta da marigayiya Stella Obasanjo, matar Shugaba Obasanjo a wancan lokacin.

A lokacin da mijinta ke mataimakin Shugaba Obasanjo, ta jagoranci kare hakkin matan da ake safararsu zuwa kasashen waje don yin karuwanci.

Ta kafa gidauniyar WOTCLEF, mai yaki da safarar mata da fafutukar ganin an kawo karshen ci da gumin yara.

Hajiya Rukaiya Atiku Abubakar, matar Atiku Abubakar ta uku

Asalin hoton, INSTAGRAM/PRINCESS_RUKAIYA_ATIKU

Bayanan hoto, Gimbiya Rukaiya, matar Atiku Abubakar ta uku

A watan Janairun 1979, Atiku ya auri matarsa ta biyu Ladi Yakubu.

Sun haifi yara shida da Ladi. Su ne Abba da Atiku da Zainab da Hauwa (Ummi) da Maryam da kuma Rukaiya.

A shekarar 1983 ya auri matarsa ta uku, Gimbiya Rukayya wacce 'ya ce ga marigayi Lamidon Adamawa, Aliyu Musdafa.

Ta haifi Aisha da Hadiza da Aliyu da Asma'u da Mustafa da Laila da kuma Abdulsalam.

Atiku Abubakar da Maryam Atiku

Asalin hoton, Twitter/@RukaiyaAtiku

Bayanan hoto, Atiku Abubakar da 'yarsa Maryam Atiku

Ya auri matarsa ta hudu Fatima Shettima a shekarar 1986.

Fatima ta haifi 'yarta ta fari Amina, sai ta haifi Mohammed sai ta yi tagwaye sau biyu Ahmed da Shehu da kuma Zainab da Aisha sannan 'yar auta Hafsat.

Rukaiya Atiku da Hafsat Atiku

Asalin hoton, TWITTER/@RukaiyaAtiku

Bayanan hoto, Rukaiya Atiku da Hafsat Atiku

Daga baya auren Atiku Abubakar da Ladi ya zo karshe, sai ya auri Jennifer Douglas (Jamila).

Jennifer 'yar daya daga cikin jihohin kudu maso gabashin Najeriya ce, kuma 'yar kabilar Ibo ce.

Haka kuma ta karanci fannin shari'a a jami'ar Washington dake Amurka.

Kuma ita ce babbar editar mujallar Miyetti Quarterly Law Review.

Jennifer (Jamila) Atiku Abubakar

Asalin hoton, InSTAGRAM/JDABUBAKAR

Bayanan hoto, Matar Atiku ta hudu Jennifer (Jamila) Atiku Abubakar

Jennifer ta haifi 'ya'ya uku da Atiku Abubakar, wato Faisal da Zahra da kuma Abdulmalik.

Atiku Abubakar da matarsa Jennifer

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, Atiku Abubakar da matarsa Jennifer

Atiku Abubakar yana da mata 4 da 'ya'ya 28.

Karin Labaran da za ku so ku karanata:

line