Buhari ya ce abu ne mai wahala ya fadi zaben 2019

Shugaban Najeriya Buhari ya ce hanyoyin yaki da rashawa da suke bi yana daukar lokaci kafin tabbatar da zargin da ake yi wa mutum.

Shugaban ya fadi haka ne a wata muhawarar tattaunawa da 'yan takarar shugaban kasa da mataimakansu da Daria Media da NTA, suka shirya tare da taimakon cibiyar MacArthur.

An tambayi shugaban ne, ko za a ga wani sabon salon yaki da rashawa sabanin tsarin da ake bi a yanzu?

Sai ya amsa cewa suna fuskantar babban kalubale musamman daga bangaren shari'a.

Dole sai dai a bi hanyar samo bayanai daga bankuna da kamfanoni domin gabatar da su a gaban kotu a matsayin shaida.

"Idan ba haka ba, ba abin da za ka iya yi," in ji shi.

Da aka tambaye shi ko kalubalen da yake fuskanta ya sanyaya masa guiwar yaki da rashawa da gwamnatinsa ke da'awa akai, sai ya ce "hakkin hukumomi ne da aikin ya rataya akansu su bi diddigin barnar da ake da kudaden jama'a."

"Ba zan nemi a sake zabe na ba kan magance tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa kuma na ce ba zan iya ba don ba ni samun hadin kai daga wani bangare."

Buhari na bincike kan kudaden kananan hukumomi

Shugaba Buhari ya ce akwai bincike da ke gudana kan gwamnonin da ke wawushe kudaden kananan hukumomi.

Shugaban ya ce ana tursasawa shugabannin kananan hukumomi su sanya hannu kan kudaden da ya kamata su zo hannunsu daga taarayya amma kuma sai a ba su kashi 25 kawai daga ciki maimakon gaba daya.

"Gwamna ne ke cinye sauran kudaden na kananan hukumomi," in ji shi.

Wani lauya daya daga cikin wadanda suka halarci zauren muhawarar Suleiman Usman Jahun ne ya tambayi shugaba Buhari kan matsalar almajirai.

Ya tambayi shugaban cewa "ko zai iya rusa tsarin almajiranci domin tabbatar da ilimi mai nagarta da alamajiran, ganin zai iya daukar mataki mai tsauri kuma ya karbu ga 'yan Najeriya kamar yadda ya kara farashin man fetur?"

Amma sai shugaban ya ce maganar almajiri shi ne matsalar tsarin ilimi a matakin farko, kuma sai idan kananan hukumomi sun iya magance matsalolinsu.

"Wannan wata dama ce ga kananan hukumomi su fito su daga murya kan matsalolinsu domin biyan bukatunsu."

"Idan ba a magance haka ba yana da wahala ga gwamantin APC ta iya magance matsalar ilimi gaba daya tun daga kananan hukumomi zuwa jiha," in ji Buhari.

Amma ya ce akwai bincike yanzu haka da ake gudanarwa a wasu jihohi inda gwamnoni ke wawushe kudaden kananan hukumomi.

Ya ce akwai wata jihar da bincike ya gano cewa ana ba shugabannin kananan hukumomi kashi 25 kawai daga kudaden hakkinsu daga tarayya sauran kuma gwamna ke wawushe wa.

Shugaba Buhari ya kalubalanci 'yan jarida su bankado yadda jiha ke bayar wa da kuma fatali da kudaden kananan hukumomi.

"Ina son a bankado yadda gwamnonin jihohi ke wawushe kudaden kananan hukumomi."

"Alhakin 'yan jarida ne a madadin mutane su shiga gudanar da binciken kwa-kwaf domin bankado irin wadannan gwamnoni da kuma shugabannin kananan hukumomi." In ji shi.

Ina tababa kan bidiyon Ganduje

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna tababa kan bidiyon da aka wallafa, wanda ke nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudade na Dalar Amurka.

Shugaban ya ce bai san irin na'urar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa bidiyon ba.

"A ce kamar gwamnan Kano yana dariya yana karbar daloli abin mamaki ne," In ji shi.

Sai dai shugaban da ke da'awar yaki da rashawa a Najeriya ya ce ya yi shiru ne bai ce komi ba game da bidiyon, kasancewar lamarin yana gaban kotu.

Wasu al'umma da kungiyoyi masu rajin yaki da rashawa a kasar sun dade suna sukar lamirin shugaban kasar na kin cewa uffan game da zargin karbar cin hancin da ake wa gwamnan.

Me za a yi da kudaden da aka kwato

Shugaba Buhari ya ce akwai tsari a shimfide kan yadda za su kashe kudaden da hukumar EFCC ta kwato.

Ya ce an samar da asusun bai-daya yadda dukkanin kudade da aka samu za su tafi.

"Za a yi amfani da kudaden ga ayyukan ci gaba musamman shinfida kwalta da layin dogo da lantarki, amma kashe kudaden zai dogara ne da kasafin kudi."

"Idan majalisa ta amince da kasafin kudi, duk gibin da aka samu za a yi amfani da kudaden da aka kwato domin cike gibin," in ji shi.

'Ba zan fadi zabe ba'

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abu ne mai wahala ya fadi zaben 2019 saboda karbuwar da ya samu.

Ya ce ya yi matukar gamsuwa da tarbar da ya samu a gangamin yakin neman zabensa a Bauchi da Kogi da sauran jihohin da ya ziyarta.

An tambayi shugaban ne, idan ya fadi zabe ko zai amince da sakamakon zaben?

Ya ce ya sha faduwa zabe. "A 2003 na kare a kotu tsawon watanni 13, a 2007 na shafe wata 18 a kotu, a 2011 na share wata takwas a kotu har kotun koli."

"Sai a karo na hudu saboda ci gaban da aka samu na samar da na'urar tantance masu kada kuri'a ya kawo karshen magudin zaben da aka saba yi," in ji shi.

Da aka tambayi shugaban kan cewa wasu na tababa game da koshin lafiyarsa da har yake neman a sake ba shi dama ya sake mulki a wasu shekaru hudu.

Sai ya amsa da cewa gangamin yakin neman zabensa ya isa ya gamsar da duk wanda ke tababa kan koshin lafiyarsa.