Yaro mai shekara 8 da ke samun dala miliyan 22 ta intanet

Asalin hoton, YouTube
- Marubuci, Daga Chris Johnston
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai aiko da rahotannin Kasuwanci, BBC News
Wani yaro mai shekara takwas wanda ke yin bayani a kan kayan wasan yara a shafinsa na YouTube ya zama na daya a jerin masu samun kudi a danadalin da dala miliyan 22.
Mujallar Forbes ta Amurka ta kiyasta cewa yaron mai suna Ryan mai shafin Ryan ToysReview ya doke Jake Paul da dala 500,000 a karshen shekarar da suka auna wadda ta kare a watan Yuni.
A kan wallafa bidiyo a kusan kowace rana, inda wani sabon bidiyon da Ryan ya fito a ciki yana tallata wani katafaren kwai ya sami masu kallonsa da suka zarce mutum miliyan daya daga Lahadi zuwa Talata.
Shafin The Dude Perfect kuma shi ne na uku da dala miliyan 20, in ji mujallar ta Forbes.
Kudaden da Ryan ya samu a bana sun nunka na bara bayan an cire haraji da kamashon da yake biyan lauyoyinsa da sauran masu yi masa hidima.
Da tashar NBC ta Amurka ta tambaye shi dalilin da yasa yara ke son kallon bidiyonsa, sai ya ce: "Saboda na iya nishadantar da su, kuma ni bai ban dariya ne".
Tun da iyayensa aka bude shafin nasa a watan Maris na 2015, bidiyon da aka wallafa an kalle su kusan sau biliyan 26, kuma shafin na da mabiya miliyan 17,300,000.
Mujallar ta Forbes ta kuma ce yana samun miliyan 21 cikin miliyan 22 ne daga tallace-talacen da a kan sanya a cikin bidiyon da a ke wallafawa, inda yake samun sauran miliyan daya kuma daga masu daukar nauyin shirin nasa.

Asalin hoton, Ryan ToysReview/Youtube
Da yake har yanzu karamin yaro ne, a kan adana wa Ryan kashi 15 cikin 100 na kudaden da yake samu a asusun ajiya a banki har zuwa lokacin da ya girma.

Asalin hoton, Ryan ToysReview/Youtube
Su ma 'yan uwan Ryan wadanda tagwayen 'yan mata ne sun rika fito wa a shafin nasa.
Sun fito a wani bidiyo da ke bayyana wa yara yadda ake gudanar da sinadarai na kimiyya, inda Ryan da 'yan uwan nasa suka fito kuma aka kalle shi fiye da sau miliyan 26.










