Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba mu da jagorori na gari — Matasa
Wasu kungiyoyin matasa a Najeriya sun koka da rashin samun jagorori nagari a siyasance wadanda za su basu damar inganta rayuwarsu ta yau da kullun.
kungiyoyin matasan wadanda suke a karkashin babbar majalisar matasa ta kasar, sun gudanar da taron su na farko, a dai-dai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasar na 2019.
Mataimakin shugaban majalisar matasan Najeriya a yankin Arewa maso gabashin kasar, Comrade Lukuman Majidadi, ya shaida wa BBC cewa, babbar matsalarsu ita ce samun jagorori nagari wadanda za su yi musu jagora wajen zama masu dogaro da kansu, ba wadanda za su rinka mayar da matasa yaran gidansu ba kawai.
Matashin ya ce, matasan Najeriya musamman na arewa suna da kishi da ilimi suna kuma da hazaka, amma samun wadanda za su yi musu jagora na gari, wadanda kuma ba za su bukaci yaran su kasance dun-dun-dun a karkashin shi ne abu mai wuya.
Comrade Lukuman Majidadi, ya ce ' Jagororinmu na siyasa a yanzu a gaskiya ba sa haska yadda matasa za su shigo a dama da su a harkokin siyasar, illa kawai su mayar da su yaransu na siyasa'.
Mataimakin shugaban majalisar matasan Najeriya, ya ce akwai hanyoyin da za a bi wajen yaye wa matasa kangin da suke ciki, ciki har da kaddamar da majalisar da za ta rinka kula da ci gaban matasa a matakin tarayya, da kuma tabbatar da cewa kudin da kowacce jiha ke warewa a cikin kasafin kudinta na shekara, a kan ci gaban matasa, to a tabbatar da cewa ana amfani da su don wadannan matasa.
Ya ce yakamata a samar da damarmaki ta yadda matasa za su rinka zuwa a gwamnatace, wato gwamnati ta rinka bayar da wani ragi ga wasu masana'antu wajen biyan haraji domin su horar da matasa sana'oi a kyauta.