Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amitabh Bachchan ya raba manoma daga kangin bashi
Shahararren jarumin fina-finan kasar Indiya Amitabh Bachchan, ya ce ya biya wa wasu manoma bashin da ya kai fiye da dala dubu 500.
Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na intanet a ranar Talata, inda ya ce manoman da ya biyawa bashin sun kai 1,398.
Kuma dukkaninsu sun fito ne daga jihar Uttar Pradesh, inda nan ne mahaifar Amitabh.
Dubban manoma a kasar Indiya dai na fama da dimbin bashi, wanda sukan jima ba su biya ba.
Bangaren aikin noma na matukar samun koma baya a kasar, inda a wasu lokutan ba a fiye samun amfanin mai gona mai yawa ba.
An kiyasta cewa tun daga shekarar 1995, manoma akalla dubu 300 sun kashe kansu a kasar ta Indiya, saboda dalilin da ke da alaka da bashin da ake binsu.
Yawanci dai manoman na ciwo bashin ne daga bankuna kasar domin su yi aikin noma, to amma wajen biya ne ake kai ruwa rana.
Wane ne Amitabh Bachchan?
Yana daya daga cikin manyan jaruman kasar Indiya da suka yi suna a duniya.
Jarumi ne kuma ya taba shiga harkar siyasa a baya.
An haife shi a ranar 11 ga watan Oktoban 1942, shekararsa 76 ke nan a 2018.
Ya fito a fina-finai fiye da 190, kazalika ya fito a fina-finan da bana kasarsa ba, wato fina-finan Hollywood.
Ya kan gabatar da manyan shirye-shirye a gidan talabijin din kasarsa wadanda mutane ke son kalla, bama a kasar ba kawai har ma da wasu kasashen duniya.
Ya auri jaruma Jaya Bachchan, inda suka haifi 'ya'ya biyu mace da namiji, namijin Abhishek Bachchan, shi ma jarumi ne, kuma ya auri jaruma Aishwarya Rai.