Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Takunkumi Amurka: Anya Iran za ta kai labari?
- Marubuci, Daga Tawagar Binciken Gaskiyar Al'amari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wasu jerin takunkumin karya tattalin arziki da Amurka za ta kakaba wa Iran sun fara aiki ranar Litinin.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya mayar da martani mai karfi.
"Babu shakka Amurka ba za ta cimma burinta ba a kan Iran domin suna ja da baya daya bayan daya."
Iran ta dogara ne kacokan kan albarkatun man da take fitarwa, saboda haka idan wadannan sabbin matakan suka yi tasiri, to tattalin arzikinta zai shiga wani mayuyacin hali.
Tarayyar Turai ta bayar da shawarar tallafa wa kamfanonin da ke cinikayya da Iran duk da wadannan jeri takunkuman.
Amma yana yiwuwa wadannan kamfanonin su fuskanci matakan ladabtarwa daga Amurka idan lamarin ya tabarbare?
Me yasa Amurka ke saka wa Iran sabbin jerin takunkumai?
Shugaban Amurka Donald Trump ya fusata da abin da ya kira "gurguwar yarjejeniya ce."
Yana magana ne a farkon shekarar nan, a yayin da ya janye daga yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Iran a 2015, wadda a karkashinta Iran din ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya domin a dage mata jerin matakan karya tattalin arzikin da kasashen duniya suka sakamata.
A saboda haka ne a 2016 Amurka da wasu kasashen suka dage dukkan takunkuman da suka saka ma Iran, amma yanzu Amurka ita kadai ke kokarin mayar da su.
Sauran kasashen duniya, wadanda suka hada da na Tarayyar Turai, na ganin Iran ta kiyaye bangarenta na yarjejeniyar makaman nukiliya, saboda haka ne suka ce ba za su saka mat ta takunkumi ba.
Amma saboda yadda Amurkar ta mamaye tsarin tattalin arzikin duniya, musamman a fagen cinikayya, sai da wasu manyan kamfanonin na kasa-da-kasa suka rika ficewa da jarinsu daga Iran.
Ta yaya takunkumin Amurka za su yi aiki kenan?
Wadannan sabbin matakan sun hana duk wani kamfanin da ke da huldar ciniki da Iran samun damar yin dukkan harkokin kasuwanci a Amurka.
Bayan wannan kuma, duk wani kamfanin Amurka da aka samu yana huldar kasuwanci da Iran zai fuskanci fushin hukuma.
Akwai kuma wasu matakan takura wa bangaren hada-hadar banki na Iran da Amurkar za ta fara aiwatar wa ranar Lintinin din.
Yadda za a kauce wa matakan Amurka
Domin samarwa kamfanonin da ke son ci gaba da hulda da Iran, Tarayyar Turai ta fitar da wani sabon tsarin ciniki da zai ba su damar kaucewa tsarin cinikayya na Amurka.
Tsarin kamar banki ya ke, inda zai rika shiga tsakanin Iran da kamfanonin a fannin kasuwanci domin ya kare su da fitar ko shigar da kudade daga kasar Iran.
A misali, idan Iran ta sayar wa wata kasar Turai man fetur, sai kamfanin da ya sayi man ya biya Iran kudadenta ta sabon asusun.
Ita kuma Iran na iya amfani da kudaden da aka zuba a wannan asusun wajen sayen kayayyakin da ta ke bukata ba tare da ta fitar da kudi daga kasarta zuwa Turai ba.