Jagoran awaren Biafra Nnamdi Kanu ya bayyana a Isra'ila

Jagoran 'yan awaren Biafra na kudu maso yammacin Najeriya Nnamdi Kanu ya bayyana a Isra'ila bayan da aka daina jin duriyarsa tun lokacin da sojoji suka kai samame gidansa.

A ranar Lahadi ne Mista Kanu ya bayyana a gidan rediyonsa na Radio Biarfra cewa, "A yanzu haka ina Isra'ila."

An rarraba wani bidiyo da ke nuna jagoran 'yan awaren Biafran yana addu'a a jikin Bangon Yamma na masallacin Kudus.

Magoya bayansa sun ce ana tsare da Mista Kanu ne tun shkarar 2017 bayan da aka kai samame gidansa.

Matarsa Uchechi Kanu ta shaida wa BBC a watan Fabrairu cewa ta yi amanna gwamnati ta san inda mijinta yake, bayan da sojoji suka kai samame gidan nasa.

Mista Kanu dai ya jima yana fafutukar neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya.

A shekarar 2015 ne aka tuhumi Mista Kanu da "hada baki wajen aikata babban laifi da razanar da mutane da kuma mallakar kungiyar da ba halattacciya ba" - laifukan da suke daidai da cin amanar kasa.

A bara ne aka bayar da belinsa bayan da ya shafe fiye da wata 19 ba tare da yi masa shari'a ba a kan tuhume-tuhumen cin amanar kasa.

Daga nan dai ya sabunta fafutukarsa ta neman 'yanci, kafin sojoji su kai samame gidansa da ke jihar Abiya.

Wane ne Nnamdi Kanu?

Mista Kanu, wanda ke da izinin zama dan kasa na Najeriya da Birtaniya, ya kirkiri kungiyar People Of Biafra (Ipob), a shakarar 2014 domin neman kafa kasar Biafra.

"Idan akwai wani bangare na Najeriya da ke son shiga yankin na Biafra, to muna musu maraba, matukar sun yi amanna da karantarwar addinan Yahudu da Kiristanci...tsarin karantarwar da kasar Biafra ta ginu a kansa.

Shirin samar da kasar Biafra dai ba sabon abu ba ne.

A shekarar 1967 shugabannin kabilar Igbo sun ayyana kasar Biafra, bayan wani mummunan yakin basasa, wanda ya jawo mutuwar kusan mutum miliyan daya, amma an samu galaba a kan masu neman ballewar.

Mista Kanu shi ne na baya-bayan nan a kabilar Igbo da ke fafutukar ci gaba da gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra.

Biafra a takaice:

  • Wani tsohon sojan Najeriya Odumegwu-Ojukwu ne ya fara ayyana jamhuriya ta farko ta neman kafa kasar Biafra a shekarar 1967
  • Ya jagoranci dakarun sojin da mafi yawansu 'yan kabilar Igbo ne a wani yakin basasa mai muni da aka shafe shekara uku ana yi, ya kuma zo karshe a 1970
  • Fiye da mutum miliyan daya ne suka rasa rayukansu, mafi yawansu saboda yunwa
  • Bayan gomman shekaru da kawo karshen rikiicin Biafra da sojoji suka yi, sai kuma kungiyoyin 'yan aware suka dinga jan hankulan matasa domin goyon bayan akidar
  • Suna jin cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta damuwa da yankin
  • Amma gwamnati ta ce korafinsu bai shafi kudu maso arewa ba.

Alaka da Isra'ila

A jawabin da ya gabatar ranar Lahadi, Mista Kanu ya ce har yanzu yana kokarin ganin an kada kuri'ar raba gardama domin yankin kudu maso gabas ya samu damar ballewa daga Najeriya.

Ya nemi magoya bayansa da su kaurace wa zaben da za a gudanar a Najeriya a 2019, har sai gwamnati ta yarda da batun kuri'ar raba gardama.

"Ipob za ta samar da kasar Biafra kuma ba za mu yi zabe ba har sai mun samu an yi kuri'ar raba gardama, ba ma bukatar sasantawa, za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da hakan," a cewar Mista Kanu.

"Kwanan nan zan dawo yankin Biafra, kuma sama da kasa za ta hade," in ji shi.

"Isra'ila ce ta tserar da ni," ya kara da cewa hukumar leken asirin kasar Mossad na matukar taimaka masa, ba tare da yin karin bayani kan yadda taimakon ya kasance ba.

Har yanzu dai ba a san ta yadda Mista Kanu ya je Isra'ila ba, saboda sanin yadda aka karbi fasfunansa na Najeriya da Birtaniya bayan da aka kama shi.