Wane ne Janar Alkali da ya bata a Filato?

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kama mutum 30 a yankin Doi Du na jihar Filato a kokarinta na neman Manjo Janar IM Alkali, wanda ya bace tun watan da ya gabata.

Tun a watan Satumba ne iyalan Janar Alkali suka sanar da labarin bacewarsa, inda suka ce ya bar gidansa da ke Abuja a ranar 3 ga watan don zuwa Bauchi inda yake da gona, amma tun daga sannan ba a ji duriyarsa ba, kuma wayoyinsa ba sa tafiya.

Ana zargin cewa an sace Janar Alkali ne wanda yake yin bulaguron a motarsa.

A ranar 29 ga watan Satumba ne kuma rundunar cika aiki da babban hafsan sojin kasa ta Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya kafa don neman Janar Alkali, ta gano motarsa a wani kududdufi da ke Lafendeg a yankin Du na karamar hukumar Jos Ta Kudu.

Rundunar sojin ta wallafa hoton motar a shafinta na Twitter.

Bayan nan ne kuma aka fara yada wani hoto a shafukan sada zumunta da muhuwara ana cewa gawar Janar Alkali ce da aka tsinto, amma rundunar sojin Najeriyar ta karyata wannan labari da kuma hoton.

A sanarwar da rundunar ta fitar ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne kuma rundunar ta yi karin bayani kan abubuwan da ta gano sakamakon ci gaba da neman Janar Alkali da ake yi.

Baya ga mutum 30 da ta ce ta kama a yankin Du, ta kuma ce ta kama manyan bindigogin gargajiya uku da kananan bindigogi uku da wukake da takubba da adduna da rodi da babura biyar da katin shaidar kungiyar 'yan sa-kai da kuma takalma sau-ciki guda biyu.

Ta kuma kara da cewa an samu keke mai kafa uku daya da kudin kasar Koriya dubu daya da agogon hannu da manyan wayoyi 25 da makullan mota biyu da mukullan gida biyu.

Sai dai har yanzu rundunar ta ce ba a ga Janar Alkali ko gawarsa kamar yadda rahotanni ke cewa an kashe shi ba, amma sojojin sun ce ana ci gaba da nemansa.

Wane ne Janar Alkali?

  • Dan asalin jihar Yobe ne
  • Ya shafe shekara 35 yana aikin soja
  • Ya yi ritaya a watan Yunin 2018
  • Shi ne babban jami'in gudanarwa na rundunar sojin Najeriya kafin ya yi ritaya

Zarge-zarge

'Yan Najeriya da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan batan Janar Alkali, inda wasu suka yi zargin cewa 'yan kabilar Berom ne suka kashe babban sojan.

Akwai kuma wani zargin da ya bullo daga wajen wani Dr Idris Ahmed wanda ke zama a Birtaniya, inda ya yi zargin cewa akwai hannun rundunar sojin kasar wajen batan Janar Alkali.

Sai dai rundunar sojin ta yi watsi da wannan zargin, inda ta kalubalanci Dr Ahmed da ya gabatar da kwararan hujjoji don tabbatar da zargin nasa.