APC ta soke zaben Zamfara a karo na biyu

A Najeriya, kwamitin zaben fitar da gwani na masu neman takarar gwamna a jam`iyyar APC ya soke zaben da aka fara a jihar Zamfara sakamakon zargin tafka magudi da tabarbarewar tsaro a lokacin zaben.

A ranar Laraba ne aka fara zaben bayan an yi ta turka-turkar kusan mako guda.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce zaben bai soku ba, kuma za ta ci gaba da gudanar da shi.

Amma ita ma uwar jam'iyyar APC ta kasa ta aike wa manema labarai wata sanarwa tana cewa an soko zaben, kuma za a sanya wata ranar ta daban domin gudanar da shi.

Kwamitin zaben, wanda ya yi jawabi ga `yan jarida a hedikwatar `yan sandan jihar Zamfara, ya yi zargin cewa akwai matsaloli da dama wadanda suka jibanci magudi da tsaro da suka dabaibaye zaben, kuma babu abin da ya fi dacewa face soke shi.

Shugaban kwamitin zaben Dr Abubakar Fari, ya yi zargin cewa akwai wasu ma'aikatan gwamnati da ma'aikatan zabe da suka karbe takardun zabe suka kuma cike sakamakon da suke so a sanar da mutane.

Dr Fari ya ce kananan hukumomin da aka samu irin wannan matsala sun hada da Talata mafara da Bakura da Maradun da Maru da Bungudu da Zurmi da Birnin Magaji sai kuma Gusau.

Shugaban kwamitin ya ce wadannan dalilai sun sanya an dage zaben sai abin da Allah ya yi, kuma hedikwatar jam`iyyar APC da ke Abuja ce kadai ke da hurumin tsayar da ranar da za a yi sabon zabe.

Amma, gwamnatin jihar ta Zamfara a nata bangaren, ta ce sam ba za ta sabu ba, inda ta zargi shugaban kwamitin da cewa dan-koren wasu daga cikin masu neman takarar ne, don haka ne ta yi fatali da matakin da kwamitin ya dauka na soke zaben.

Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya ce zabe bai soku ba, hasali gwmnati za ta dora daga inda kwamitin zaben ya tsaya ba tare da bata lokaci ba.

To sai dai kwamitin koli na uwar jam'iyyar APC ta kasa ya ce an soko zaben, kuma nan ba da jimawa ba za a sanya wata ranar gudanar da zaben.

Masu neman takara na cikin wadanda suka jikkata a je-ka-ka-dawon da aka yi ta yi sakamakon daddage zaben.

Masassharar da ke damun zaben fitar da gwanin jihar Zamfara dai za a iya cewa ta ki jin magani, musamman ma idan aka yi la`akari da cewa an so a yi zaben da takardun kada kuri`a abin ya gagara.

Kana an jarraba `yar tinke ita ma ta haifar da tankiya, wadda a karshe an yi rabuwar da ba rakiya tsakanin bangaren gwamnatin jihar da `yan kwamitin zaben.