Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
APC ta hana ministocin Buhari biyu takarar gwamna
Jam'iyya mai mulki a Najeriya APC ta fitar da jerin sunayen mutanen da ta tantance masu son tsayawa takarar gwamna a jihohin kasar, sai dai ba ta tantace wasu minsitocin gwamnati biyu da ke son tsayawa takarar ba.
Ministocin dai sun hada da Barista Adebayo Shittu na ma'aikatar sadarwa wanda ke takarar gwamnan jihar Oyo da kuma Aisha Jummai Alhassan ministar mata, wacce ke takarar gwamnan jihar Taraba.
Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce ba ta tantance Barista Adebayo ba ne daga cikin 'yan takarar gwamna takwas na jihar, saboda rashin shaidar yi wa kasa hidima da ba shi da ita.
Tuni dai Mista Shittu ya yi murabus daga kujerarsa don tsayawa takarar gwamnan.
Amma sanarwa ba ta bayyana dalilin da ya sa ba a tantance Aisha Jummai Alhassan a matsayin 'yar takarar gwamnan Taraba ba daga cikin mutum 12 da suke takarar.
Sai dai za a iya tuna cewa Aisha Alhassan ta nuna mubaya'arta ga Atiku Abubakar, wanda ake ganin ubangidanta ne a siyasance, kan goyon bayansa a takarar shugabancin kasar nan, tun kafin ya koma jam'iyyar PDP mai adawa.
Wannan dalili ne ya sa ake ganin jam'iyyar APC na iya kin tantance ministar, ko da yake dai jam'iyyar ba ta yi wani karin bayani kan dalilin rashin tantance ta din ba.
A baya-bayan nan ne dai ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta yi murabus sakamakon gano cewa ta yi jabun takardar yi wa kasa hidima.
Al'amarin dai ya jawo ce-ce--ku-ce da dama a kasar inda wasu suka dinga kira cewa a tsige ta, wasu kuma na ganin ba wani laifi ne da ya kai ta yi murabus ba.