Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fara aiwatar da umarnin Osinbajo kan SARS
Sufejo janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya sauya tsarin tafiyar da rundunar yaki da fashi da makami ta SARS bisa umarnin da mukaddashin shugaban kasar ya bayar ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sandan kasar, Jimoh Moshood ya fitar ranar Talata, Idris ya nada kwamishina wanda zai yi ta lura da rundunar, wadda yanzu aka saka mata suna rundunar tarraya ta yaki da fashi da makami (FSARS).
Sufeto janar na 'yan sandan ya ce a yanzu za a hade dukkan rundunonin FSARS din na fadin Najeriya a karkashin kwamishinan 'yan sanda daya.
Wannan na zuwa ne sa'o'i bayan mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayar da umarnin yin garambawul a hukumar gudanarwa da kuma ayyukan rundunar 'yan sanda ta musamman mai yaki da fashi da makami (SARS) a kasar.
Mukaddashin shugaban Najeriyar ya ba da umarnin ne bayan korafe-korafen take hakkin bil Adama da aka yi wa rundunar ta SARS.
Sanarwar 'yan sandan ta ce sufeto Janar din ya ce dole kwamishinonin 'yan sanda a fadin kasar su bi umarnin, ta hanyar yi wa sauran jami'ansu gargadi kan badda kama da sunan su ma 'yan rundunar FSARS ne.
Ta kuma kara da cewa daga yanzu rundunr za ta yi aiki kamar yadda doka ta tsara, tare da mutunta 'yancin wadanda ake zargi kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Domin cimma wannan ma'aikatar 'yan sanda za ta samar da bangaren kula da hakkin bil Adama ga rundunar FSARS a ko wacce jiha domin jin korafe-korafe daga mutane, wadanda za'a tura ga hedikwatar 'yan sanda, kuma 'yan sandna wannan bagaren za su yi aiki ne da kwamshinan 'yan sanda mai kula da FSARS a hedikwatar, maimakon kwamandan FSARS a jiha.
Haka kuma nan take za a fara nazari kan tunani da lafiyar jami'an FSARS din.
Za kuma a sake fasalin kakin jami'an FSARS a fadin kasar na take
Sannan daga yanzu, jami'an FSARS ba za su yi aikin binciken abubuwan hawa ba, sai dai in an nemi a kawo dauki kan laifukan fashi ko kuma garkuwa da mutane.
Cikin 'yan kwanakin nan dai matasa a Najeriya sun yi ta neman a soke rundunar a shafukan sada zumunta, musamman ma Twitter ta hanyar amfani da maudu'in #EndSARS .
A ranar Talata ce dai wata sanarwa da babban mai taimakawa na musamman na mukaddashin shugaban kasar kan harkar watsa labarai, Laoulu Akande ya fitar, ta ce duk wata rundunar da za ta fito bayan garam bawul din za ta mayar da hankali ne kawai kan aiki da bayanan sirri da hanawa tare da gano fashi da makami da satar mutane, gami da kama wadanda da suka yi irin wadannan laifukan.
Hakazalika Osinbajo ya umarci sufeto janar na 'yan sanda ya tabbatar da cewar dukkan jami'an da za su kasance cikin sabuwar rundunar su zama masu gudanar da ayyukansu ta hanyar mutunta dokakin kasa da kuma kiyaye hakkin bil Adama na wadanda ake zargi da aikata laifi.
Mukaddashin shugaban kasar ya kuma ce dole ne jami'an rundunar su ringa tafiya da alamar rundunar a duk lokacin da suke bakin aiki.
Har wa yau, Osinbajo ya umarci shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya da ya samar da wani kwamiti na musamman wanda zai yi bincike game da zargin da ake yi wa rundanr SARS na yin wasu ayyuka ba bisa doka ba, domin mutane su samu damar gabatar da koke-kokensu.