Tsoron Buhari ya sa ake fita daga APC - El-Rufa'i

Bayanan sautiKalaman Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce wasu na fita ne daga jam'iyyar APC saboda tsoron wa'adin mulkin shugaba Buhari na biyu.

El-Rufa'i wanda na hannun dama ne ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadi wasu dalilai guda uku zuwa hudu da ya ce su ne suka sa wasu 'ya'yan jam'iyyar APC ke ficewa daga Jam'iyyar.

Gwamnan ya ce wasu na ganin shugaba Buhari kwanto ya yi a wa'adin mulkinsa na farko bai kakkama duk barayi ba.

"Kadan ya kama amma suna ganin a wa'adinsa na biyu zai koma ne ya sa kakin soja ya kama dukkanin barayin dukiyar gwamnati ya kulle su."

"Suna jin tsoro idan aka bar shi ya kai wa'adi na biyu ga abin da zai ma su." In ji El-Rufa'i yayin wata ganawa ta musamman da kafafen yada labarai a jihar Kaduna.

A makon da ya gabata ne, 'yan majalisar tarayya sama da 50 suka fice daga APC zuwa jam'iyyun adawa.

'Yan majalisar dattawa 14 da kuma na wakilai 38 suka sanar da ficewarsu daga APC, inda mafi yawa suka sanar da komawarsu babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Baya ga 'yan majalisar, akwai kuma gwamnonin APC da suka fara ficewa da kuma karin wasu da ake ganin suna kan hanyar ficewa daga jam'iyyar da ke mulki a Najeriya.

Wadanda suka sauya shekar daga APC zuwa wasu jam'iyyun na adawa sun ce sun fice ne saboda rashin jin dadin yadda gwamnati ke tafiyar da al'amuranta da yadda ake tafiyar da uwayen gidajensu, da kuma halin da kasa take ciki, ana ta kashe-kashe da sace-sacen mutane.

El-Rufa'i ya ce sun dade da sanin za ta kai ga haka domin asalin jam'iyyar APC hadi ne na gambiza, jam'iyyu ne da dama suka hadu suka kafa APC.

"Wasu sun shiga jam'iyyar ne saboda sun ga alamun za ta ci zabe amma ba don Allah suka shigo jam'iyyar ba."

"Yawancinsu karuwan siyasa ne, yau suna wannan jam'iyyar gobe suna wannan domin abin da suke nema shi ne ace kullum suna cikin gwamnatin jam'iyyar da za ta ci. Ba ruwansu da baka ce ko fara ce, shudiya ce, za su shiga."

Ya ce suna ficewa ne daga jam'iyyar saboda ba su yarda da akidar APC ba da kuma akidar shugaba Buhari, domin sun shigo ne ba don Allah ba ko don talaka.

El Rufa'i tare da Shugaba Buhari

Asalin hoton, @nasirelrufai

Bayanan hoto, El Rufa'i ya ce wadanda ke ficewa APC karuwan siyasa ne

"Idan jam'iyya ta balaga ta fara girma to wadanda ba su yi daidai da ita ba za su koma inda suka fito, kuma babu wanda yake son ya yi siyasa kuma yana son ya saci kudin jama'a ya so shugaba Buhari," in ji El-Rufa'i.

Ya kuma ce "kashe-mu-raba da mutane suka saba da shi ba shi ne tsarin APC ba kuma ba shi ne tsarin Buhari ba, saboda haka ne wasu za su duba su ga cewa ashe sun yi kuskuren shigowa APC, za su ce gara mun tafi inda ya fi daidai da mu."

El-Rufa'i ya ce sun dade suna jin wasu na cewa "kai! wannan jam'iyyar mutum ya shiga ya yi wahala an ci zabe amma har yanzu ba mu samu komi ba."

Gwamnan na Kaduna ya kuma ce akwai wadanda suka fice saboda suna son kujera kuma suke ganin yanzu ba za su samu ba.

Ya ba da misali da rikicin siyasar Kaduna tsakanin shi da su Sanata Shehu Sani da kuma Sule Hunkuyi wadanda ya ce "tun da aka fara tafiyar APC idonsu yana kan kujerar gwamnan Kaduna."

"Idan suka diba suka ga cewa babu dama ko kuma ni ina son in sake neman kujerar kuma kila suka diba suka ga shugabannin jamiyya na jihar Kaduna sun ga ba zai yiyu ba, to ka ga kila hakan zai sa su tsallake.

El-Rufa'i ya ce tun kafa gwamnatinsa suke yaki da shi saboda daya daga cikin dalilai guda hudu ko uku da ya zayyana.

El Rufa'i tare da Shugaba Buhari

Asalin hoton, @nasirelrufai

Bayanan hoto, El Rufa'i ya ce sun san wadanda ko a gidansu aka yi zabe ba za su ci ba.

Ya kuma ce irin wannan rikicin ne ya mamaye sauran jihohin da jam'iyyar APC ke mulki.

Sai dai ya amsa cewa wannan babbar baraka ce ga jam'iyyaar APC musammam saboda zaben da ke tafe a badi.

"Ina da tabbacin cewa sabon shugaban jam'iyyarmu na kasa Adams Oshiomhole ya san yadda zai yi maganin wadannan matsalolin."

Masharhanta salon siyasar Najeriya na ganin ficewar 'yan majalisa da kuma wasu gwamnonin APC, babban al'amari ne da zai iya raunata matsayin Shugaba Muhammadu Buhari a majalisar dokoki, kuma wata babbar barazana ce ga takararsa a zaben 2019.