Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wata mata ta bar jaririn da ta haifa a jirgin sama
An tsare wata mata bayan an tsinci gawar wani jariri a cikin jirgin sama wanda ya tashi daga Guwahati da ke arewa maso gabashin Indiya zuwa babban birnin Delhi.
Ma'aikatan kamfanin jirgin sama na Air Asia ne suka tsinci jaririn lokacin da jirgin zai sauka a ranar Alhamis.
Sun tambayi dukkanin matan da ke cikin jirgin kuma wata mata mai shekara 19 ta amince cewa ita ce ta haife shi a cikin jirgi.
'Yan sanda sun fada wa BBC cewa matar ta ce ba ta ma san tana dauke da juna biyu ba.
Yanzu haka 'yan sandan sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike.
Babban jami'in 'yan sanda Sanjay Bhatia ya shaida wa BBC cewa matar ta haifi dan tayi ne dan wata 7 da rabi a ban-dakin jirgin kuma ta bar shi a kasa.
Ya kara da cewa 'yan sandan suna jiran sakamakon bincike domin gano yadda jaririn ya mutu.
Mr Bhatia ya ce za su san abin da ya faru tare da daukar matakan da suka kamata bayan sakamakon binciken ya fito.
An hana matar wadda 'yar wasan taekwondo ce shiga jirgin da zai wuce kasar Korea ta kudu.
Kamfanin na Air Asia ya fitar da wata sanarwa inda yake ba pasinjojinsa hakuri kan tangardar da aka samu.
"Kamfanin zai ci gaba da bincike tare da tuntubar masu ruwa da tsaki," a cewar sanarwar.
A yanzu haka 'yan sandan na kokarin tuntubar dangin matar da ke Assam.