'Rikicin makiyaya ya fi na Boko Haram illa'

Rikicin makiyaya da manoma

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kungiyar ta dora alhakin rikicin kan gazawar gwamnati wajan gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu

Wani sabon rahoto kan rikici tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya ya ce adadin mutane da suka rasa rayukansu ya ninka sau shida na yawan wadanda suka mutu a rikicin Boko Haram.

Kungiyar International Crisis Group (ICG) da ke kokarin hana barkewar yaki ta ce mutum 1,300 ne suka hallaka a tashe-tashen hankulan da suka faru a yankin tsakiyar Najeriya tun daga watan Janairu.

Binciken ya kuma ce mutane 3000 ne suka rasa matsugunansu.

Rahoton ya kuma ce akwai batutuwa da dama da suka haddasa rikicin ciki har da sauyin yanayi da filayen noma da aka fadada.

Sai dai kungiyar ta ICG ta ce tashin hankalin da ya faru a 2018 ya biyo bayan karuwar da aka samu na yawan mayakan sa-kai na kabilu da suka mallaki makamai ta bayan fage.

Ta kuma dora alhaki a kan gazawar gwamnati wajan gurfanar da wadanda ake zargi a gaban shari'a da kuma dokar hana kiwo da aka zartar wadda makiyaya da dama sun nuna rashin amincewarsu akanta.

Rahoton ya yi gargadi kan cewa tashin hankalin kan iya komawa rikicin da ke da nasaba da addini da kuma kabilanci saboda akasarin makiyaya Musulmi ne ya yin da manoma yawancinsu Kirista ne.