Ethiopia da Eritrea sun ayyana 'karshen yakinsu'

Asalin hoton, @HAWELTI
Shugabannin Ethiopia da Eritrea sun rattaba hannu kan takardar da ta ayyana cewar "yanayin yakin da ya kasance tsakanin kasashen biyu ya zo karshe", kamar yadda ministan watsa labaran Eritrea ya wallafa a shafin Twitter.
Ba a taba aiwatar da cikakkiyar yarjeneiyar zaman lafiyar da ta kawo karshen yakin kan iyaka tsakanin kasashen biyu daga shekarar 1998 zuwa 1999 ba.
Tun wannan lokacin ne dai ake zaman dar-dar tsakanin kasashen masu makwabtaka.
Sanarwar ta fito ne bayan wata ganawa ta tarihi tsakanin shugabannin kasashen biyu a babban birin kasar Eritrea, Asmara.
Ganawar tsakanin shugaban kasar Eritrea, Isaias Afewerki, da kuma Fraministan Ethiopia, Abiy Ahmed, ita ce ta farko tsakanin shugabannin kasar kasashen cikin kusan shekara 20.
Ranar Litinin, shugabannin sun yarda cewar "an shiga wani sabon lokaci na zaman lafiya da kawance", kamar yadda ministan watsa labaran Eritrea, Yemane Gebre Meskel, ya fada a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X







