Zaki ya cinye masu farautar karkanda a Afirka ta Kudu

Zakuna sun kashe akalla mutum biyu masu farautar karkanda a wurin kula da namun daji da ke kasar Afirka ta Kudu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Jami'ai masu kula da namun daji ne suka gano ragowar gawawwakinsu wadanda ake kyautata zaton na mutum biyu ko uku ne a wani wuri da zaki yake da iko a wurin kula da namun daji na Sibuya da ke kusa da garin Kenton.

An kuma gano wata babbar bindiga da aka tsinta a kusa da wurin.

Ana samun karuwa yawan masu fataucin namun daji a nahiyar Afirka shekarun baya-baya nan saboda yawan bukatar da ake yiwa kahon karkanda a wasu sassan nahiyar Asiya.

Kasashen China da Vietnam da sauran wurare, sun yi amannar cewa za'a iya yin amfani da kahon karkandar wajen yin magani.

Mutumim da ya mallaki wurin Nick Fox a cikin wata sanarwa da aka walafa a shafin wurin kula da namun dajin ya ce mutane wadanda ake zargin mafarauta ne sun shigo wurin ne a daren ranar Lahadi, ko kuma safiyar ranar Litinin.

"Sun fada tarkon zaki - kuma suna da yawa sosai shi ya sa mutane ba su iya tserewa ba," kamar yadda Mista Fox ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Ba mu san adadin mutanenn ba - saboda abin da zakunan suka rage kadan ne."

A ranar Talata da misalin karfe 14;30 na agogon GMT ne aka gano kasusuwan mutanen.

Jami'ai masu yaki da masu farauta sun je wurin, inda suka gano bindiga da adda da kuma igiyar da masu farauta suke amfani da ita domin cire kahon karkanda.

Sai da aka yi ma wasu daga cikin zakunan alurar barci kafin aka kwashe kasusuwan mutane, kamar yadda Mista Fox ya ce.

'Yan sanda sun rika sintiri a yanki domin duba yiwuwar ko za'a samu wani daga cikin masu farautar da ya tsira.

A bana karkanda tara mafarauta suka kashe a lardin gabashin Cape, inda a nan ne wurin namun dajin yake.

An kashe karkanda fiye da dubu 7,000 a kasar Afirka ta Kudu a cikin shekaru 10 da suka wuce.