Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli hotunan shugaban Faransa a gidan rawa a Legas
Ga wasu zababbun hotuna na Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, yayin da ya kai ziyara gidan rawa na marigayi Fela Kuti da ke birnin Legas, don tunawa da zamanin da yake zuwa a lokacin da yake matashi.
A ranar Talata ne Shugaba Macron na Faransa ya isa Najeriya, inda ya fara ya da zango a Abuja don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.
Daga bisani kuma sai ya wuce birnin Legas a ranar, inda da daddare ya ziyarci fitaccen gidan rawa da aka gina don tunawa da shahararren mawakin nan Fela Kuti.
Fela dai ya mutu ne a shekarar 1997, kuma fitaccen mawaki ne da aka san shi da dabi'ar neman mata da shaye-shaye da rashin tsoron sukar gwamnatocin mulkin soji.
Yana kiran kansa da lakabin "Shugaban kasar bakar fata."
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato shugaban Faransan a lokacin da yake kan dandamalin rawa yana:
"Fela ba mawaki ba ne kawai. Dan siyasa ne da ya so ya sauya al'umma. Don haka idan ina da sako daya ga matasa, to bai wuce wannan ba; 'Eh, siyasa na da muhimmanci, kwarai, don haka ku shiga a dama da ku."
Reuters ta ce, kasancewar Mista Macron a wajen ya sa gidan rawar ya yi armashi sosai fiye da ko yaushe.
Babu warin wiwi kamar ko yaushe kuma babu irin matasan nan da ke taruwa a wjaen gidan rawar ko yaushe, saboda irin tsananin tsaron da aka sanya a gidan lokacin ziyarar shugaban.
Shugaba Macron wanda ya taba shafe wata shida a matsayin mai sanin makamar aiki a ofishin jakadancin Faransa da ke Najeriya a shekarar 2000, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, cewa tun a wancan lokacin yake son Najeriya.
"Kasa ce mai shiga rai. Akwai abubuwan da nake tunawa da su sosai... wadanda har yanzu ban manta ba."
A yayin ziyarar Shugaba Macron gidan rawar an yi ta sanya wakokin Fela, inda mutane daban-daban suka yi ta rawa, an kuma yi tallan kayan kawa.
Mista Macron ya yi ta wallafa bidiyon ziyarar tasa gidan rawa na Fela Kuti a shafinsa na Twitter, yana mai cewa hakan ya tuna masa karkashin mutanen Afirka da ya gano tun zamansa a Legas yana dan shekara 23.
Mista Macron ya ce ya yi farin ciki sosai da ya ga har yanzu mutane na cike da karsashi, yana mai cewa "hakan ya sha bamban da labaran bakin ciki da nahiyar Afirka ke fuskanta."
Ya kuma ta daukar hotuna da tarurarin fina-finan Nollywood.
Macron ya shaida wa manema labarai cewa Najeriya na da muhimmanci ga al'adun Afirka.
Gabanin isar sa Legas dai, Mista Macro ya tsaya a Abuja don ganawa da Shugaba Buhari, inda suka tattauna a kan sha'anin tsaro.