Mayakan BH 32 sun mika wuya

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram akalla 32 sun mika wuya ga dakarun kasar a yankuna daban-daban na arewa maso gabashin Najeriyar.
Rundunar ta wallafa hotunan mutanen da ake zargi mayaka ne, sai dai bata ce ga wani shiri ko yadda za a yi da su ba.
Kiyasi ya nuna cewa mayakan Boko Haram sama da 200 ne suka ajiye makamansu a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Na baya-baya nan da aka samu shine wanda ke zuwa, bayan dakarun Najeriya sun yi ikirarin kashe mayaka 5 a cikin karshen mako.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadi dubban rayuka a arewacin Najeriya bayan raba miliyoyi da matsugunansu.







