Shin Kwankwaso zai iya doke Buhari a zaben 2019?

Mun samu dubban ra'ayoyin jama'a bayan wallafa labarin da Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi ikirarin cewa shi ne mutumin da ya fi kowa karfi da farin jinin da zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

A karshen makon jiya ne tsohon gwamnan jihar Kanon ya shaida wa fitaccen dan jarida kuma mawallafi, Dele Momodu shi yanzu ba shi da wata jam'iyya, amma PDP ce ta fi kowacce dama da karfin kayar da shugaban, idan har ta ci gaba da bin tafarkin demokradiyya.

Yayin da Shugaba Buhari bai ce komai game da batun ba, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, wanda tsohon abokin tafiyar Kwankwason ne a siyasa, ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne.

"Kwankwaso ba zai iya lashe zabe a mazabarsa ba, ballantana ya iya kayar da Shugaba Buhari," in ji shi.

Haka ma dai sauran jama'a suka rika ci gaba da bayyana mabambantan ra'ayoyinsu game da kalaman sanatan da kuma martanin Gwamna Ganduje musamman a kafofin sada zumunta a kasar.

'Kwankwaso yana kiran kasuwa ne'

Mun tuntubi masanin kimiyyar siyasa na Jami'ar Abuja Dokta Abubakar Kari wanda ya ce "idan aka ce siyasa ko kuma zabe, babu yadda za a yi wani ya ce wani abu zai yiwu ko kuma ba zai taba yiwu ba."

Ya ce: "saboda harkar zabe tana da daure kai kwarai da gaske. Sai an tambayi wane ne Kwankwaso, wane ne Buhari, mene ne tarihin siyasarsu, wace irin dama suke da su da dai sauransu. Kafin a san ma ci tuwo."

Malamin jami'ar ya ce shi ganinsa batun waye zai ci zabe, ko waye ba zai ci ba, "yana fito wa fili ne idan ya rage 'yan makonni kafin zabe."

"Ni abin da na fahimta shi ne Kwankwaso yana kiran kasuwa ne, wato yana tallata kansa ne. Yana so ne jam'iyyar PDP ta yi zawarcinsa kuma ta ba shi damar yin takarar shugaban kasa."

Dokta Kari ya kara da cewa: "Mutumin da ke ikirarin zai ci zabe a karkashin wata jam'iyya kuma bai ma shiga jam'iyyar ba har yanzu, sannan kuma saura kimanin watanni biyu kafin a yi zaben fidda gwani, ai ka ga abin akwai daure kai ke nan."

Hakazalika jama'a shafukanmu na Facebook da Instagram sun rika tafka muhawara, yayin da wadansu suke ganin Kwankwason ba zai iya doke Buhari ba, wasu suna ganin hakan mai yiwuwa ne.

Sunusi Garba Muhammad cewa ya yi: "BBC ku rubuta ku ajiye idan dai ba a yi gyara a gwamnatin Baba Buhari ba, to fa Kwankwaso zai iya fyada Buhari da kasa, ganin yadda yake da magoya, a lungu da sakunan Najeriya. Fatan mu Allah ya zaba mana mafi alheri."

Shi ma Lawan Adam Muhammad cewa ya yi: "A cikin ruwan sanyi Kwankwaso zai kada Buhari saboda Kwankwaso shi ne dan takarar da zai iya lashe zabe a jihohi 20 ba tare da bata lokaci ba."

Sai dai ra'ayin Kabir Najeeb Gwarzo ya sha bamban:

"Abin dariya wai yaro ya tsinci hakori. Ai Kwankwaso ko a Kano bazai iya doke Buhari ba, balle kuma a Najeriya. Wannan oyoyo din da ya ga Yarbawa na masa shigo-shigo ba zurfi ne saboda Yarbawa sun fi son Buhari ya koma mulki saboda su amsa a 2023, domin idan Kwankwaso ya zama shugaban kasa, ta tabbata yankin arewa zai yi shekara 12 yana mulki ke nan."

Muhammad Auwal: "Allah shi ne masani amma ai ya san cewa ba zai hada kansa da Buhari ba, saboda duk wanda ya riga ka barci to dole ya riga ka tashi, san nan ruwa ba sa'an kwando ba ne".

Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - za ku iya bayyana naku ra'ayoyin a shafin namu na Facebook:

Masu neman takara a PDP kawo yanzu

  • Atiku Abubakar
  • Ayo Fayose
  • Ahmed Makarfi
  • Sule Lamido
  • Malam Ibrahim Shekarau
  • Kabiru Tanimu Turaki
  • Sanata Datti Baba-Ahmad