Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta samu Joshua Dariye da laifin almundahana
- Marubuci, Abdulwasiu Hassan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Wata babbar kotu a Najeriya ta samu tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye da laifin almundahana da halatta kudaden haram.
Mai shari'a Adebukola Banjoko ta samu Mr Dariye, wanda sanata ne da ke wakiltar Filato ta tsakiya, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 daga cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.
Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.
Nan gaba kadan ne za a yanke masa hukunci.
Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da wata kotu ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.
Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.
Mai shari'a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.
Lauyansa Kanu Agabi ya soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari'ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.