'Gwamna yana limanci amma ana kashe bayin Allah a Zamfara'

An yi ta yin ce-ce-ku-ce game da wani bidiyo da muka wallafa a shafinmu na Facebook, inda Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari yake limancin sallar Magriba.

Gwamnan yana limancin ne a gidansa da ke garin Talatar Mafara a jihar Zamfara, inda wadansu sarakun gargajiya da kwamishinonin jihar suke halarta lokacin buda baki.

BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukan sada zumunta bayan wallafa bidiyon a shafinta na Facebook.

Wasu 'yan kasar sun bayyana jin dadinsu bayan ganin bidiyon, yayin da wadansu suke nuna rashin jin dadinsu.

Mustapha Kabiru Masha: "Allah haka ake so shugabanin su zama, amma kuma yana da kalubale a kansa saboda ana zubar da jinin al'umma a jiharsa babu wani abu da yake yi a zahiri."

Nasir Maina Suleiman: "Ana kashe bayin Allah bai damu ba. To me ye amfanin limancin da yake. Tun kan a haife shi ake limanci. Kai wannan yaudara ce."

Sai dai ra'ayin Mu'hd Sani Ahmad ya sha bamban:

"Yayi kyau, haka akeson shugabanci ta kowanne bangare ace mutun yananan. Allah Yakarbi Ibadarmu."

Mun tuntubi Daraktan Watsa Labarai na Gwamnatin jihar Aminu Ibrahim Gusau, wanda ya ce "kashe-kashe ba zu hana yin sallah ba don ko wajen yaki ana yin sallah."

"A duk lokacin da gwamna ya kammala jan sallar yana yi wa jama'a wa'azi kan su koma wa Allah. Kuma gwamnatin tana bakin kokarinta wajen kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa."

Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohin Najeriya da suke fama da barazanar tsaro.

Ko a makon jiya wasu 'yan bindiga masu fashin shanu sun sake afkawa wani kauye a jihar Zamfara, inda suka kashe a kalla mutum 23 a ranar Juma'a.

Rahotanni sun cewa daruruwan mutanen Kauyukan Zamfara ne ke gudun hijira a yanzu domin tsira daga yawaitar kashe-kashen da ake yi.

Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - kuma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na Facebook:

Karanta wadansu karin labarai