Fiye da dalibai 50 sun kamu da kwalara a wata makaranta a Kaduna

Asalin hoton, FACEBOOK KADUNA STATE GOVT
Cutar amai da gudawa ta bulla a wata makarantar kwana ta 'yammata a cikin jihar Kaduna ta Najeriya, inda rahotanni ke cewa har dalibai biyu sun rasu.
Cutar dai ta kara kamari ne a safiyar ranar Litinin a makarantar GGSS Kawo.
Rahotanni sun ce kimanin dalibai sama da 50 ne suka kamu da cutar a makarantar.
Tuni dai aka garzaya da wadanda suka kamun zuwa wani babban asibiti a Kadunan.
Kwamishinan ilimi na jihar, Alh Jafaru Sani, ya tabbatar wa da BBC cewa, kimanin dalibai 55 ne suka kamu da cutar ta kwalara a makarantar.
Alhaji Jafaru ya ce, ba a yi wata-wata ba aka kwashesu aka kai su asibitin Kawo da ke jihar.
Kwamishina ya ce, daliba daya ce ta rasu a cikin wadanda suka kamu da cutar, akasin yadda ake rade-rade cewa dalibai biyu ne.
Alhaji Jafaru Sani ya ce, cutar ta bulla ne sakamakon karancin wutar lantarki da aka shafe kwana uku ba bu a makarantar sai aka rasa ruwa sha dana sauran amfani a makarantar.
Ya ce hakan ya sa daliban suka fara zuwa wata rijiya da ke kusa da wani rafi a kusa da makarantar suna dibar ruwa.
Kwamishinan ya ce, suna kyautata zaton a wannan ruwan rijiyar ne saboda ba shi tsafta sosai suka sami cutar.

Karin bayani akan cutar kwalara
A kan kamu da cutar da kwalara sakamakon ta'ammali da gurbataccen ruwan sha da abinci ko kuma kazanta.
Jihohi da dama a Najeriya ne ke fama da bullar amai da gudawa inda har hukumomin lafiya na duniya suka kaddamar da riga-kafin cutar wadda suka ce za ta karade kasashe da dama na Afirka.











