Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan auren Yarima Harry da Meghan Markle
An daura auren Yarima Harry da Meghan Markle, auren da aka dade ana jira.
An daura auren ne a Windsor inda ma'auratan suka yi wa juna alkawali tare da sanya wa juna zobe.
An gudanar da auren ne a gaban Sarauniyar Ingila da kuma baki 600 da aka gayyata.
Daruruwan mutane ne suka halarci bikin daurin auren, yayin da miliyoya suka kalli bikin kai tsaye a Talabijin
Yanzu Yarima Harry da amaryarsa Meghan za a kira su da sarautar Duke da Duchess na Sussex.
Ga wasu daga cikin hotunan bikin auren da aka gudanar a ranar Asabar.