Boko Haram: Sojin Najeriya sun sake kwato mutum 1,000

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sake kwato mutum fiye da 1,000 daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Ta kara da cewa yawancin mutanen da aka kwato mata ne da yara da kuma samari da aka tilastwa zamowa mayakan kungiyar.

A jerin sakonnin da ta wallafa a shafinta na Twitter, rundunar sojin ta ce an ceto mutanen ne, wadanda suka fito ne daga kauyukan Karamar Hukumar Bama a jihar Borno, da taimakon dakarun kasa da kasa da ke yaki da kungiyar.

An yi amannar cewa Boko Haram ta kama dubbban mutane a shekaru taran da ta shafe tana tayar da kayar baya, kuma ba wannan ne karon farko da sojoji ke ikirarin kubutar da jama'a ba.

Babu hotuna ko wata shaida da sojojin suka fitar kawo yanzu, kuma babu bayani ko akwai 'yan matan makarantar nan ta Chibok da aka sace shekara hudu da ta wuce a cikin wadanda aka kwato din.

Wannan shi ne karo na uku a cikin wata hudu da suka gabata da sojin ke ikirarin kwato mutane daga hannun Boko Haram.

Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun karya lagon kungiyar amma har yanzu tana kai munanan hare-hare musamman na kunar bakin-wake a yankin arewa maso gabashin kasar.

Dubban mutane ne suka mutu a rikicin na Boko Haram, yayin da sama da mutum miliyan biyu suka rasa muhallansu.