Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon yadda harin masallacin Mubi ya yi mummunar illa
Akalla mutum 28 ne suka mutu wasu sama da 50 kuma suka jikkata a harin da aka kai wani msallaci a birnin Mubi na jihar Adamawa.
Harin ya yi mummunar illa ga masallacin da kuma wasu dukiyoyi da ke kusa da shi.
An dauki lokaci mai tsawo ba a kai hari a birnin na Mubi ba da ma sauran sassan jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin Najeriya.