Guterres ya roki Trump kan shirin nukiliyar Iran

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya roki Amurka da kada ta janye daga yarjejeniyar kasashen duniya kan takaita shirin nukiliyar kasar Iran.

Mr Guterres ya shaida wa BBC cewa yankin gabas ta tsakiya na cikin yanayi mai matukar hadarin shiga yaki matukar ba'a mutanta yarjejeniyar ba.

A shekarar 2015 ne kasar Iran ta amince ta yi matukar rage shirinta na nukiliya inda daga bisani kasashen duniya suka janye akasarin takunkumin tattalin arzikin da aka sanyawa kasar.

Sai dai shugaba Donald Trump na ganin Iran ba ta cika wasu daga cikin alkawuran da ta yi ba inda ya yi barazanar janye goyon bayan Amurka nan da wasu kwanaki.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yarjejeniyar babban nasara ce da aka cimma ta fuskar diflomasiyya kuma wajibi a kiyaye ta.

Kasashen turai da ke kawance da Amurkar na fatan shawo kan Mr Trump domin ya ci gaba da sa ido kan yarjejeniyar ta hanyar amincewa da sabbin matakai da suka hada da farmakin makami mai linzami.

Sai dai wasu jami'an diflomasiyya na kasashen yamma na fargabar cewa shugaba Trump ka iya yin biris da rarrashi Mr Guterres da kuma kamun kafa na wasu shugabannin kasashen turai.