Sojoji sun dakile harin Boko Haram a Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile wani hari da mayakan Boko Haram suka yi yunkurin kaiwa birnin Maiduguri na jihar Borno.

Rahotanni sun ce da yammacin ranar Alhamis ne mazauna birnin suka yi ta jin karar harbe-harben manyan bindigogi.

Lamarin dai yasa wasu mazauna birnin sun dimauce har ta kaiga wasu mutane tserewa daga gidajensu.

Sai dai wani jami'i a hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno ya shaida wa BBC cewa yanzu haka al'amuran sun koma kamar yadda suke bayan an dakile yunkurin harin.

Wannan ne dai karo na biyu cikin wata guda da mayakan Boko Haram ke yunkurin kutsa wa cikin birnin amma sojoji suna fatattakar su.

Ko a farkon watan Afrilu sai da aka kashe mutum goma sha biyar a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a birnin.