Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boko Haram: An kashe mutane a masallaci a Borno
Akalla mutane shida ne suka hallaka a wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a garnin Bama, a jiahr Borno da ke arwa maso gabashin Najeriya.
Mutanen da suka mutu sun hada da mahara biyu mace da namiji, da kuma masallata hudu.
Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno Ya Bawa Kolo ta shaidawa BBC cewa wasu mutanen kuma sun ji rauni, kuma tuni aka garzaya da su asibiti.
Hukumomin jihar sun ce an kai harin ne lokacin da ake sallar asuba.
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma dai kungiyar Boko Haram tana yawan kai irin wadannan hare-hare a yankin.
Hukumomin Najeriya na ikirarin samun galaba a kan kungiyar Boko Haram, to sai dai kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan arewa masu gabas, musamman ma a jihar Borno.
Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Najeriya gami da raba sama da mutum miliyan biyu da mahallansu.