Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jami'ar OAU za ta binciki farfesan da ya nemi dalibarsa
Hukumomin Jami'ar Obafemi Owolowo da ke garin Ile-ife ta ce ta kafa wani kwamitin domin bincikar sahihancin wata hirar waya da aka nada wadda aka ace tsakanin wani malamin jami'ar ne da wata daliba.
A cikin hirar an ji namijin ya nemi macen ta amince ya yi lalata da ita har sau biyar domin ya kara mata makin da zai sa ta ci jarrabawa saboda ta fadi.
An ce dalibar ce ta nadi hirar da malamin mai mukamin farfesa kuma ta yada ta a shafukan sada zumunta, wacce jama'a ke ta ci gaba da yada wa.
Kakakin Jami'ar Abiodun Olanrewaju ya BBC cewa sun gano ko wanene farfesa ne. Amm ba sa su fadi sunansa a kafar watsa labarai.
Kawo yanzu malamin da ake zargi bai ce komai ba.
"Lallai ni ma na saurari wannan hirar kuma mun iya tabbatar da wani abu a ciki. Amma ba mu son mu tafi gaba-gadi mu yanke hukunci.
Don haka tsangayar nazarin harkokin gudanarwa ta kafa wani kwamiti da zai duba batun kuma ya gano ainihin wadanda suka yi hirar" in ji Abiodun Olanrewaju.
Mr Olanrewaju ya ce hukumar jami'ar ta nemi farfesan ya yi bayani kan lamari, kuma zai bayar da amsa a kan rubutacciyar tambayar da aka aike masa.
Ya kara da cewa akwai kuma kwamiti da jami'a ta kafa na wasu sanannun masu gaskiya, wadanda za su duba wannan zargin da ake yi masa kamar yadda dokokinmu suka tanada.
Sai dai duk da cewa hukumomin jami'ar sun yi ikirarin cewa sun dauki mataki kan lamarin, akwai dalibai da yawa a shafukan internet da ke cewa wannan abin ba yau yake faruwa ba.
Daliban sun yi korfin cewa hukumomin jami'ar ba sa daukar matakan kare su.
Sai dai hukumomin sun ce suna daukar mataki idan wani ya zo ya fada mu su an ci zarafin wata.
Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami'oin Najeriya.