Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Kamaru sun tsere daga wasannin Commonwealth
'Yan wasan Kamaru kimanin takwas sun yi batan-dabo a wasannin Commonwealth da ake gudanarwa a kasar Australia.
'Yan wasan na daga cikin 'yan wasa 24 na tawagar kasar da ke samun horo a Warwick kafin su tafi zuwa Gold Coast, inda ake gudanar da wasannin na Commonwealth.
Uku daga cikinsu 'yan wasa masu daukar abu mai nauyi ne, sauran 'yan wasa biyar da suka yi layar-zana 'yan dambe ne.
Yanzu dai an sanar da 'yan sandan Australia a kan batun, sannan an wallafa sunayen 'yan wasan da ba a san inda suka yi ba.
Bayanai sun nuna cewa shida daga cikin 'yan wasan na Kamaru sun yi wasa a gasar, yayin biyu kuma suka yi batan-dabo.
Wadansu bayanai sun ce takardun izinin shiga kasar na biza da aka bai wa 'yan wasan zai daina aiki ne daga ranar 15 ga watan Mayu.
Shugaban kwamitin shirya gasar Peter Beattie ya ce za a tasa keyar duk wani dan wasa zuwa gida bayan karewar bizarsa.
Jami'in hulda da jama'a na tawagar kasar Kamarun, Simon Molombe ya ce hukumomin kasar sun ji takaicin bacewar 'yan wasan, tare da bayyana fatan za su dawo masaukinsu domin su koma gida tare da sauran 'yan tawagar.
A shekarar 2012 ma wadansu 'yan wasan Kamaru bakwai sun yi batan-dabo a lokacin wasannin Olympics da aka gudanar a birnin Landan.
Shugaban kwamitin shirya wasannin Commonwealth a Australia, Peter Beattie ya ce suna da masaniyar cewa biyar daga cikin 'yan wasan Kamaru ba su halarci wasannin da ya kamata su yi ba.
"Kawo yanzu ba su yi wani laifin da ya shafi bizarsu ba" a cewarsa Mista Beattie
Tun a ranar Lahadi ne dai 'yan wasa uku suka bar masaukinsu cikin dare, sannan a ranar Litinin aka nemi wasu karin biyu aka rasa kafin da dare wasu karin uku suka yi batan-dabo.
Hukumar shirya gasar ta ce tana ci gaba da sa ido a kan batun.
'Yan wasa na da damar fita zuwa duk inda suke so muddin suna da cikakkiyar biza.
Mista Beattie ya ce za su tabbatar da sun taso keyar duk wani dan wasan da ya ci gaba da zama kasar bayan bizarsa ta kare zuwa gida ba.