An hana 'yan agajin kungiyar Izala sa inifom a Nijar

Rundunar 'yan sandan jihar Maradi a Jamhuriyar Niger ta nemi da 'yan agajin kungiyar Izalatul Bid'a Wa Ikamatussunnah na jihar da su dakata da sanya kayan sarki na agaji har zuwa wani dan lokaci.

Sulaiman Hashimu shugaban 'yan agajin a jihar Maradi ya shaida wa BBC cewa sun samu sako ne daga 'yan sandan jihar, inda aka ce an dakatar da su daga sanya kayan inifom na agaji.

"Jami'an tsaro na 'yan sanda ne suka bayar da umarnin. Mun tambaye su dalilin hakan sun ce su ma ba su san dalili ba umarni aka ba su daga sama," in ji Malam Hashimu.

Ya kara da cewa tuni suka bi wannan umarni, "duk da cewa ba a gaya mana dalili ba amma uwar kungiya ta ce mu bi umarnin da jami'an tsrao suka ba mu."

Sulaiman Hashimu ya kuma ce za su saurara zuwa wani dan lokaci don ganin ko za a gaya musu dalilin daukar wannan mataki.

"Idan kuma aka dauki lokaci ba a gaya mana dalili ba to ba wani abu da za mu iya yi da kanmu dole sai abun da uwar kungiya ta kasa ta ce, don da umarninta za mu yi amfani," a cewarsa.

BBC ta tuntubi hukumomin jihar Maradi don jin matsayarsu kan wannan batu, amma sun ce ba su da bayanin da za yi wa namema labarai a yanzu.

Sai dai sun ce za su tuntubi manema labaran nan gaba kadan.

Yawanci dai an san cewa 'yan aikin agaji na kungiyar Izala kan saka inifom a Najeriya da Nijar, wanda da shi ne ake bambance su da sauran jama'a saboda irin aikin da suke yi na agaji a lokutan da ke wau manyan taruka na kungiyar, ko kuma ranakun Juma'a da sallah da kuma wa'azi.

Karanta karin wasu labarai: