Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria: Sarakunan Zamfara za su nemi agajin MDD
A Najeriya, wasu shugabannin al'umma a jihar Zamfara sun ce za su nemi Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika wajen kawo karshe matsalar tsaro da ta addabi al'umma a jihar.
Daya daga cikin manyan Sarkaruna a jihar, mai martaba Sarkin Zamfara Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad shi ne ya bayyana haka a hira da ya yi da BBC.
Sarkin wanda aka kashe gomman mutane a masarautarsa ya ce za su yi hakan ne idan matakan da hukumomin jihar suka dauka yanzu suka kasa magance matsalar.
A ranar Jumu'ar da ta gabata ne dai gwamnan jihar ya ce ya ba jami'an tsaro umarnin harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga a jihar.
Sai dai wasu masana shari'a sun soki matakin da gwamnan jihar ya dauka inda suka ce ya sabawa dokar kasar.
A kwanakin baya ne wani dan majalisar dattawan da ke wakiltar jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.