Saudiyya ta bai wa Nigeria dala miliyan 10 don 'yaki da ta'addanci'

Gwamnatin Saudiyya ta bai wa Najeriya tallafin dala miliyan 10 domin yaki da masu tayar da kayar baya a kasar.

Tallafin na Saudiyya dai wani bangare ne na shirin Sarki Salman na samar da ayyukan agaji ga wadanda rikici ya shafa.

A ranar Litinin ne Ministan Tsaro na Najeriya Mansur Dan-Ali ya bayyana hakan yayin da ya tarbi tawagar Masarautar Saudiyyar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ministan Tsaro na Saudiyyar Mr. Nasir Mutbak ya ce an bayar da tallafin ne don samar da abinci da sauran kayan bukatu a sansanonin 'yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin kasar.

"Mun zo nan ne domin gabatar da sakon Sarki Salman na taimakon 'yan uwanmu da ke sansanonin 'yan gudun hijira a arewa maso gabas, mun zo nan ne don mu taimaka musu. Kuma tabbas mun kawo gudunmowar dala miliyan 10," a cewar Mr Mutbak.

Minsitan Tsaron Najeriya ya tabbatar da cewa tabbas za a yi amfani da tallafin yadda ya dace wajen yaki da ta'addanci a kasar.

Gwamnatin Saudiyyar ta kuma jaddada aniyarta ta hada gwiwa da Najeriya don shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.