Kalli hotunan masu maitar kallon fina-finai a sinima a India

An kwashe sama da shekara 70 ana nuna al'adun India a sinima inda ake nuna fina-finai ga masu kallo a yankunan kasar daban-daban.

Suna nuna fina-finai a matsayin wani ɓangare na ayyukan addini da na nishaɗi ga miliyoyin mutane.

Ana buga manyan tantuna a bayan manyan motoci kuma ana nuna fina-finai ta amfani da majigi.

Amma ci gaban fasaha ya sa irin wadannan gidajen kallon sun fara rasa masu zuwa, wadanda suka fi son kallon fina-finai a faifan DVD da wayoyin hannu.

Amit Madheshiya wanda ya lashe lambar yabo a wurin daukar hotona, ya fara kirkiro shahararrun gidajen kallon fina-finai na Indiya a shekara ta 2008.

Ga dai wasu daga cikin hotunan da ya dauka:

Amit Madeshiya ya fara aiki a kan aikin majigi na tafi da gidanka a farkon shekarar 2008.

Lokacin ne wuraren kallo masu majigi daya da dama suka rufe.

Amit ya ce lokacin da ya ga yadda mutane ke son kallin fina-finai a sinima, sai ya fara aiki da Shirley Abraham inda suka yi ta tagfiye-tafiye a cikin kasar.

Mutane na shagala sosai a yayin da suke kallon fina-finai a sinima a Indiya.

Amit ya ce a cikin shekarun nan ya lura cewa mutane da dama na matukar son zuwa kallo sinima, kuma hakan na hada kan mutane duk da bambancin harshe da addini.