Israel ta gargadi Iran bayan ta kai hare-hare a Syria

Asalin hoton, AFP
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kasarsa za ta kare kanta daga abin da ya kira "dukkan hare-hare" bayan da ta kai wasu jerin hare-haren a wasu wurare dake cikin kasar Syria.
Isra'ilar ta kai hare-haren ne bayan da ta ce ta dakile wani hari da aka akai mata da jirgin sama mai sarrafa kansa ta kan iyakar Syria da kasar ta Isra'ila.
Iran ta musanta zargin.
Matuka jirgin sun sami kubuta da rayukansu amma akwai rahotannin da ke cewa an kai su asibiti.
Ana ganin wannan ne karo na farko tun 2006 da Isra'ilar ta rasa jirgin yakinta ta fagen daga.

Asalin hoton, AFP
Mista Netanyahu ya ce Isra'ila ba za ta amince da duk wani yunkuri da Iran za ta yi ba domin ta fadada ikonta na soji a Syria.
Amma ya kuma ce kasar Isra'ilar na bukatar "zaman lafiya da makwabtanta", a yayin wata ganawa da ya yi manyan hafsoshin sojin kasar.

Asalin hoton, AFP







