Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Obasanjo yana shirin kafa wata kungiyar siyasa ne?
Akasarin jami'an gwamnati da masu sharhi kan budaddiyar wasikar da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari sun fi mayar da martani ne kan kiran da ya yi cewa kada Shugaban ya sake tsayawa takara a 2019.
Watakila hakan ba ya rasa nasaba da tsammanin da ake yi cewa, kamar sauran shugabannin da suka gabace shi, Shugaba Buhari zai so sake yin takarar karo na biyu ko da yake har yanzu bai bayyana sha'awarsa kan hakan ba.
Sai dai daya daga cikin manyan batutuwan da suka fito fili a wasikar shi ne bukatar da ya nuna ta kafa sabuwar gamayyar kungiyoyi da za ta kawar da jam'iyyar APC da PDP daga mulki.
"Me za mu yi idan APC da PDP ba su kai Najeriya gaci a wannan mawuyacin halin ba?
"Kamar yadda wani Farfesa a Jami'ar Kennesaw ta Amurka Farooq Kperogi, ya fada, "zabin da ke gabanmu na da wahala; tamkar ka ce ne zabi tsakanin shaidanu biyu. Babu wani bambanci.
"Ba za mu nade hannu mu zauna muna ta kokawa ba...Muna bukatar gamayyar kungiyoyi, ba kawai jam'iyyar siyasa ba, wacce kowanne dan Najeriya nagari zai iya shiga."
Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa yana fatan gamayyar kungiyoyin za ta zama wata hanya ta fitar da Najeriya daga kangin da take ciki.
Gabanin wannan wasika dai, wasu 'yan kasar da dama sun yi kira a samar da wata kungiya da za ta kawar da APC da PDP daga mulki.
Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili na cikinsu, inda ta fito da wani maudu'i ma taken #RedCardMovement da ke da zummar zaburar da 'yan Najeriya su yi fatali da jam'iyyu irinsu APC da PDP sanna su kafa kungiyar da za ta maye gurbinsu.
A cewarta, hakan ne kawai zai sa 'yan kasar su kafa gwamnatin da za ta kula da su kana ta yi ayyukan ci gaban kasa.
Sai dai wani Malamin da ke nazari kan harkokin siyasa a Jami'ar Abuja, Dr Abubakar Kari, ya shaida wa BBC cewa da wahala a samu irin wannan kungiya a Najeriya.
Ya ce Najeriya kasa ce da ba a cin zabe ba tare da an shiga wata jam'iyyar siyasa ba, don haka ko menene zai faru, ya zama wajibi ga masu rajin kafa gamayyar kungiyar su sani cewa bukatarsu ba za ta biya ba sai sun koma kan turbar da aka sani.
Da alama dai za a ci gaba da yin muhawara kan wannan batu har zuwa zaben 2019 - ko ma bayansa - kuma masana na ganin hakan a matsayin ci gaban dimokradiyya.