Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wata likita na son a halatta kaciyar Mata
Wata likita a Kenya ta shigar da bukatar neman kotu ta halatta kaciyar mata a kasar, inda ta ce kariya ce ga lafiyarsu.
Likitar mai suna Tatu Kamau ta shaidawa jaridar Daily Nation ta Kenya cewa ya kamata matan da suka balaga a ba su 'yancin yin duk abinda suka ga damar yi da jikinsu.
"Kamar yadda ake kokarin kare yara mata, amma akwai mata da yawa da aka gallazawa kuma aka daure a gidan yari shekaru uku da suka gabata", a cewar Dakta Kamau.
Ta kara da cewa, da zarar mace ta kai shekarun balaga, ita ba ta ga dalilin da za a ce ba za su iya daukar irin wannan mataki ba.
Likitar ta shaidawa Kotu cewa ba tana magana ba ne game da yara mata, illa tana yaki ne domin kare mutuncin 'yancin mata.
Likitar ta kuma shaida wa manema labarai bayan ta fito daga kotun cewa halatta kaciyar ta mata inda ake cire wani sashe na al'aura, kariya ce ga lafiyarsu.
Dakta Kamau ta ce haramta kaciyar mata ya sabawa al'adun mutanen Afirka da dama, kuma al'amari ne da ya kamata a sake dubawa.
Jaridar Standard ta ruwaito cewa, wata sabuwar doka da aka kafa a 2011, ta haramta kaciyar mata, dokar da ta kunshi dauri a gidan yari tsakanin shekara uku zuwa daurin rai da rai.