Yadda ake shagali da kwari a wasu kasashe

Sau da dama ana kwatanta Kwarin da ake ci a matsayin wani abinci da ke gina jiki, wanda kuma ya fi dacewa ga muhalli sabanin dabbobi. To Amma wadanne irin mutane ne ki cin kwarin, ko suna da dadi a baki kuwa?

Wasu mutum biyu sun boye a cikin wani tamfal sun daure kansu da wata igiyar tsumma a yayin da suke kokarin yadda za su kama gidan rina. Sun dade suna jiran irin wannan lokaci.

Sun bi dubaru da dama ta yadda za su tafi da gidan rinar.

Bayan sun shafe tsawon sa'a biyu suna kafa tarko da kai hari domin kama rinar, a wani daji da ke tsakiyar Japan, daga karshe mutanen biyu sun samu biyan bukata.

Mutanen biyu sun dawo gida dauke da daruruwan rina da yawansu ya kai kilogram bakwai.

A kwalaben giya suna fitar da sauran Rina daga gidanta, matansu kuma na tafasawa da ruwan zafi, kuma yana da dadi kamar nama idan aka ci danyensa amma ya fi dadi idan aka soya da citta da man waken soya.

Suna soya kananan Rinar har sai ta soyu, kamar nama.

Makwabta dai na kawo ziyara domin kwarin da ake hada wa da ruwan giyar da aka hada daga ruwan da aka sarrafa Rinar.

Kamar yadda suke jin dadin kwarin, suna shammatar juna kan wanda zai dade yana bacci a daren da aka yi bushasha da kwarin.

Suna dai danganta Rina a matsayin babban maganin da ke kara karfin maza.

A sassan da dama ana fuskantar irin haka, inda mutane ke fita suna kamun kwari, ba wai don suna cikin rashin jin dadi ba sai don yadda suke jin dadin cin kwarin.

Kamar misalin tsutsar Tequila, tana jan hankalin 'yan yawon bude ido. wato wata nau'in tsutsa da ake saka wa a kwalba, da ya kasance abinci da ake matukar kauna a Mexico.

Ana samo tsutsar ne a kasan wani bishiriyar fulawa, kuma tsutsotsin da ake samu sun banbanta daga bishiyar.

Jar tsutsar ta fi tsada, saboda ta fi dadi da kamshi.

Ana matukar bukatarsu, lamarin da ya sa ake takaita lokacin cirar tsutsar. Amma a duk lokacin da mutum ya kai ziyara kasuwar Oaxacan zai ga ana tallar jar tsutsar.

Yawancin kwarin da ake ci, ba su da wahalar samu, domin da yawancinsu suna sauka ne daga sama. kamar misalin Gara, ana cin ta a mafi yawancin kasashen Afirka da ke kudu da sahara.

Bayan ruwan sama na farko, ana ganin wasu kwari sun fito kamar hayaki.

Washegari kuma za a ga dubbansu a kasa.

Yawanci yara ne suke fita su kama.

Ana dafa su, a gyara da gishiri a ci.

An fi cinsu a yankunan karkara, amma ana samunsu kuma a kasuwannin birane inda ake sayar da su nan take.

Yawancin kwarin da ake ci na girma ne a kan itacen bishiya.

Idan ka kai ziyara kudancin Burkina Faso a lokacin damina, za ka samu Kwazima ta lullube gayyen bishiya.

Kauyawa na buga sammako domin kwasar tsutsar da suke amfani da ita a miya a madadin nama, ko kuma a soya don marmari.

Wasu na girma ne a cikin itacen bishiya, kamar wadanda ke rayuwa a cikin itacen giginya.

Ire-irensu an fi samunsu a Jamhuriyyar dimokuradiyar Congo, inda masu saran itace ke amfani da gatari su bare itacen domin fitar da kwarin da ke rayuwa a ciki.

Ana gasa nau'in kwarin ne a wuta, kamar yadda ake gasa naman daji.

Kwarin da aka fi ci yawanci sun hada da Fara da Tsanya da Gyare.

Sauran kwarin sun hada da Rina da Zanzaro da Gwazarma da suka kasance abincin alfarma ga wasu.

A yankin Asia, manoma na amfani da raga a filin noman shinkafa domin kama Fari.

Haka ma a Mexico ana amfani da bokiti domin kama fara a filin noman masara.

Ya fi sauki fiye da cin nama, kuma ya fi amfani fiye da naman ruwa, domin suna da dadin ci.

Kamar amfanin gona, yawancin kwarin da ake ci ma suna da kakarsu, inda ake gudanar da bukukuwan tsintarsu a wasu sassan duniya, da suka kunshi bikin wasp a Japan da bikin caterpiller a Burkina Faso da kuma Jamhuriyyar dimokuradiyar Congo.

Kokarin tabbatar da kwari a matsayin abincin yau da kullum, na ci gaba da bunkasa musamman imanin da aka yi suna tattare da sinadarai masu gina jiki.

Kwarin da yanzu haka mutane kimanin biliyan biyu ke ci, ana ganin sun fi dacewa da muhalli maimakon dabbobi.