Jagoran Hamas ya harbi kansa bisa kuskure

Kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta ce daya daga cikin manyan jami'anta ya harbi kansa bisa kuskure.

Kakakin kungiyar Fawzi Barhoum ya ce jagoran ya harbi kansa ne a gidansa lokacin da yake duba lafiyar bindigar.

Wasu majiyoyin asibiti sun ce Imad al-Alami yana karbar magani a wani asibiti da ke Gaza.

Shi dai tsohon mamba ne mai kula da bangaren siyasa a kungiyar kuma yana da alaka ta kut da kut da Iran.

Babu tabbaci kan musabbabin harbin, sai dai da farko wasu rahotanni sun nuna cewa mai yiwuwa ya yi yunkurin kashe kansa ne.

Mista Alami, mai kimanin shekaru 60 da ake wa lakabi da sunan Abu Hamam, yana daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Hamas.

A shekarar 2003 Amurka ta ayyana shi a matsayin wani dan ta'adda kuma mamba a kungiyar Hamas da ke zaune a Damascus babban Syria.

Haka kuma ta ce shi ne ke kula da ayyukan soji na kungiyar a Gaza da kuma yammacin Jordan.

A shekarar 2014 an taba bada rahoton an raunata Mista Alami a kafarsa inda aka yi masa tiyata a kasar Turkiya.

An yi ta rade-radin cewa an ji masa rauni ne a rikici tsakanin mambobin Hamas.

Sai dai kungiyar Hamas ta ce ya ji rauni ne a wani harin da Isra'ila da ta kai ta sama, lokacin yaki tsakanin Israila da mayakan Hamas a Gaza.