Boko Haram: Abubuwa uku da Shekau ya fada a sabon bidiyonsa

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fito a wani faifan bidiyo inda ya ce kungiyarsa ce ta kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.

Bidiyon mai tsawon minti 31 da dakika 53 ya nuna shugaban Boko Haram din sanye da farar riga tare da bindiga a jingine a kafadarsa.

Shekau dai ya yi magana ne cikin harshen Larabci da Hausa kuma ya karanta da yawa daga cikin maganar da ya yi da harshen Larabci ne daga cikin wata takarda rike a hannunsa.

Da yake karatu daga cikin takardar ya yi ta runtsa ido, abin da ke nuna cewa ba ya ganin abin da yake karantawa sosai.

Ba za a iya tabbatar da lokacin da aka dauki sabon bidiyon na Boko Haram ba.

Mu muka kai hare-hare.

Shugaban Boko Haram ya ce mayakansa ne suka kai hare-hare a Maiduguri da Damboa da Gamboru.

Sannan ya ce suna nan lafiya ba abinda ya same su.

Bidiyon ya nuna harin da Boko Haram ta kai wani shingen binciken sojoji a kauyen Molai da ke kusa da Maiduguri a ranar kirsimeti, harin da sojoji suka ce sun murkushe mayakan kungiyar bayan shafe lokaci mai tsawo suna musayar wuta.

An nuna 'yan Boko haram rike da manyan bindigogi, wasu cikin budaddiyar mota wasu saman babur suna harbi amma ba tare nuna wadanda suke musayar wutar da su ba.

Bidiyon ya nuna yadda mayakan suka kwashi makamai da motocin sojoji da na gwamnatin Borno.

Martani ga Janar Rogers

A cikin bayaninsa, Shekau ya ambaci sabon shugaban rundunar Operation lafiya Dole da ke yaki da Boko Haram, Manjo-Janar Nichola Rogers, wanda ya yi kira ga 'yan Boko Haram su tuba.

Shugaban na Boko Haram ya mayar da martani inda ya ce kwamandan sojin Najeriyar ne ya kamata ya tuba.

Sannan ya ce ba abin da Sojoji da 'Yan sanda za su iya yi akan su.

Birnin Kudus

Shekau ya tabo batun Birnin Kudus, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya amince a matsayin babban birnin Isra'ila.

A cikin bayaninsa, ya ce Falasdinawa da ke ikirarin 'yan kishi ne da gangan suke yi.

"Ba da gaske suke ba, inda da gaske suke da ba za su bari wani ya karbi masallaci ya je yana abin ya ga dama ba" a cewar shugaban na Boko Haram.

Sannan ya soki Saudiya a matsayin kasar da ke shawara da Yahudawa.

Boko Haram har yanzu dai barazana ce.

An shafe watanni Shekau bai fitar da bidiyo ba, lamarin da wasu ke dangantawa da cewa alamu ne na karya lagon kungiyar Boko Haram.

Bidiyon na zuwa ne kwana daya bayan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a sakonsa na sabuwar shekara ya ce dakarun kasar sun samu galaba a kan 'yan Boko Haram.

Sai dai har yanzu Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga tsaron Najeriya da kasashen da ke makwabta da ita.

Tun da farko dai rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile harin da Boko Haram ta kai a Molai a ranar Kirsimeti.

Kwamandan rundunar Lafiya Dole Janar Nicholas Rogers ya ce dakarun sojin sun yi bata-kashi da mayakan Boko Haram bayan da suka farma wani wurin binciken sojoji da ke wajen birnin Maiduguri.

.