Buhari ya bayar da kwangilar hanyar Abuja-Kaduna-Kano

Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayar da kwangilar hanyar Abuja-Kaduna-Kano wadda rashin bayar da kwangilar gina ta ta janyo wa gwamnatinsa suka a baya.

A wata zaman majalisar zartarwar kasar da aka yi tsakanin ranar Laraba zuwa ranar Alhamis ne aka bayar da kwangilar wadda aka bayar kan kudi naira biliyan 155 da miliyan 700.

Ministan ayyuka da gidaje da wutar lantarki, Babatunde Raji Fashola, ne ya fitar da sanarwar bayar da kwangilar.

Fashola ya ce majalisar zartarwar ta bayar da kwangilar babbar hanyar da ta tashi daga Efire zuwa Araromi da Aiyede da Aiyela wadda za ta hada jihar Ondo da ta Ogun akan kudi naira biliyan 14 da miliyan 400.

Har wa yau an gyara yawan kudin da za a kashe wa hanyar Inugu zuwa Anacha ta bangaren yankin Amansiya a kudu maso gabashin Najeriya.

Majalisar ta amince da ta bayar da kwangilar aikin hanyar da ke yankin Umunya a kudu maso gabashin Najeriyar kan Naira biliyan 23 da miliyan dari 400.

Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta sha suka a baya game da irin abin da ya yi wa al'ummar jahar Kano, jahar da ta fi ba shi kuri'u a zaben da aka yi a shekarar 2015.